1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cika shekaru 10 da fara haƙo man fetur a Cadi

Mohammad AwalOctober 10, 2013

Sai dai bayan shekaru goma na aikin har yanzu ƙasar na daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya duk da ma cewar tun da farko Bankin Duniya da ta ba da kuɗaden aiki ta yi tsamani kwaliya za ta biya kuɗin sabulu.

https://p.dw.com/p/19xYz
Die Fotos stammen von Christof Krackhardt und wurden im Februar 2011 im Auftrag der Arbeitsgruppe Tschad (einer Arbeitsgruppe aus Misereor, Brot für die Welt, Diakonie-Team Menscenrechte, Amnesty International, urgewald, EIRENE und dem Bonner Forschungszentrum BICC). Alle Bilder wurden gemacht, um die Schäden für Menschen und Umwelt durch das Erdölförderprojekt unter der Konsortialleitung von Esso im Süden des Tschad (Doba-Becken) zu dokumentieren.
Hoto: Christof Krackhardt

A farkon shekarun 1990 a yankin kudancin na Cadi kafin a fara haƙo man fetur ɗin a bisa kasuwanni za a iya sami kayan gona da na lambu waɗanda suka haɗa da albasa,da tumatri,da dai sauransu sannan kuma sha'anin kiwo ya yi albarka ta yadda za a iya samin shanu da sauran dabobi sannan kuma ga wasu kayayyaki da su kan iso a yankin daga ƙasashe maƙofta irinsu Najeriya da Kamaru. A wannan lokaci da a birnin Ndjamena babban birnin ƙasar babu inda ke da titi mai tsada ko kwalta abin da ya sa yin balaguro sai an yi kwanaki biyu a kan hanya kafin a isa.

To amma tun lokacin da Kamfanin Exxon Mobil na Amirka ya fara aikin na tono man, jama'a a yankin suka saka rai cewar wata sabuwar rayuwa za ta samu. Yousouf Banengone na daga cikin sarakunan yakin wanda ya bayyana fatan cewar a lokacin sun yi fata na gari kamfanin zai kawo musu sauyi. Ya ce :''Muna jiran Esso ta gina mana makarantu da asibitoci da rijiyoyi da kuma hanyoyi a cikin ƙauyuka.'' Waɗannan sune irin kallamun da basaraken ya bayyana tun lokacin da aka fara aikin.

Fatan samar da ilimi da ruwan sha da kuma kula da lafiyar al'umma.

Nach der Ernte Bauwollverladung von Hand in der Nähe von Léré, Region Mayo-Kebbi West. Copyright: Albrecht Harder 02.04.2009, Léré
Masu aiki kaɗa a Mayo-Kebbi da ke a yammacin ChadiHoto: Albrecht Harder

Wannan shi ne fatan da ita ma gwamnatin ta ke da shi tun can da farko, wanda ministan samar da man fetur na ƙasar ya sanar da cewar kasafin kuɗaɗen gwamnatin zai ƙaru da kishi 50 cikin ɗari a wannan kataɓaren aiki wanda kamfanin na Esso ya saka kusan bilyan uku na Euro. Daman dai ƙungiyoyin masu fafutuka da masu kare muhali sun yi gargaɗin cewar Cadi ba ta da ƙwarewa da masaniya a kan irin waɗannan mayan ayyuka, Domin babu wani sahihin tsari na demokraɗiyya da zai iya tantance yawan kuɗaɗen shiga na gwamnatin. Waɗanda kuma suke ganin cewar har yanzu ba a rabu da buƙar ba a kan sha'anin yaƙi da talauci. Djeralar Miankeoel wani dan ƙungiyar gwagwarmaya ya yi garagaɗi da daɗewa a kan wannan batu.

Ya ce :'' Mutane sun rasa filayensu na noma a cikin shekaru biyar zuwa goma su kan iya kasancewa cikin wani hali na Rashi.''

Shirin aikin na haƙon man fetur ɗin da Bankin Duniya ta riƙa tinƙaho da shi.

Bankin Duniya wacce ita ta ba da kuɗaɗen tallafin samar da wannan arziki da zumar samin sauyi na rayuwar al'umma ta fannin gina makarantu da hanyoyin mota da kyautata sha'anin muhali da aikin gona. Ta cimma wata yarjejeniya da gwamnatin ƙasar ta Cadi tun da farko cewar ta saka kishi 70 cikin ɗari na kuɗaden wajen yaƙi da talauci, yayin da kishi biyar ya kamata a sakasu ta hanyar samar da ababban more rayuwa ga yankin na kudanci inda ake hako man. To sai dai yau bayan shekaru goma ƙungiyoyi masu fafutuka sun ce gwamnatin ta karya wannan yarjejeniya domin kuwa al'umma ba ta amfana ba da arzikin. Djeralar Miankeoel na ɗaya daga cikin wakilai na ƙungiyoyin masu fafutuka na ƙasar. Ya ce:'' Mutane sun sa rai so sai na samin ci gaba ta hanyar samin cikkaken sauyi na rayuwa suna tunani da man fetur ɗin 'yan Cadi za su iya ciyar da kansu, su tura ya'yansu zuwa makarantu kana su sami ruwan sha na fompi mai kyau. Amma yau shekaru goma idan ka je ka duba saɓanin haka ne kawai ke faruwa''

Chadian soldiers form a line with their armoured vehicles in the northeastern town of Kidal, Mali, February 7, 2013. Around 1,000 troops from Chad led by the president's son advanced towards the mountains of northeast Mali on Thursday to join French search-and-destroy operations hunting Islamist jihadists. Picture taken February 7, 2013. REUTERS/Cheick Diouara (MALI - Tags: POLITICS CIVIL UNREST CONFLICT)
Sojojin Cadi a MaliHoto: Reuters

Babu izini ga jama'a na yin tsokaci a kan batun man fetur ɗin inji wakilai na ƙungiyoyi masu fafutuka.

Ana zargin cewar dangin da 'yan uwan shugaban ƙasar sune ke cin moriyar arzikin man fetur ɗin ta hanyar kwangilolin da suke samu, sannan kuma ba biyan buƙata ga gine-gine da hanyoyin da gwamnatin ke yi waɗanda ba su da inganci, kana kuma yawancin kuɗaɗen da ake samu ta hanyar man gwamnatin makamai take saya Delphine Djiraibe wata lauya kuma mai fafutuka ta ce, da sake a kan wannan lamari.Ta ce: ''Ko hanyoyin da ake ginawa kafin wa'adinsu ya cikka sun lalace, kuma ai sai a duba a ga waɗanne kamfanoni ke samin wannan kwangiloli na gine-ginen,yawancinsu kamfanoni ne mallakar ƙana shugaban ƙasar.''

Anwältin Delphine Djiraibe setzt sich für Menschenrechte in Tschad ein. Der tschadische Menschenrechtlers Djeralar Miankeoel , Mitbegründer und Leiter des Vereins Ngaoubourandi.
Delphine Djiraibe da Djeralar Miankeoel wakilai na ƙungiyoyi masu fafutuka a ChadiHoto: DW und Martin Petry

To sai dai da yake mayar da martanin ministan sadarwa na ƙasar ta Cadi Hassan Sylla Bakari ya ƙaryata zargin cikin fushin a lokacin wata fira da DW kana kuma ya ƙara da cewar gwamnatinsu ta yi kyakyawar ayyuka. Ya ce: ''A shiga cikin lunguna na ƙurya na ƙasar Cadi za a ga irin ayyukan da gwamnati ta yi kama daga makaratun da asibitoci da manyan filayen saukar jiragen sama a garuruwa da dama, irin su Ndjamena da Abeche da sauransu.'' Kuma a lokacin da DW ta ke yin hira da shi minista ya fusata ya dakatar da hirar a kan tambayar da aka yi masa dangane da alƙaluma da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar a shekarun 2012 kan cewar duk da man fetur ɗin amma Cadi na fama da talauci ta yadda ita ce ta 184 cikin ƙasashe 187. Yanzu haka dai a ƙasar ta Chadi jama'a ba su da ikon yin furci a kan harkokin tattalin arziki na ƙasar musamman man fetur wanda nan da nan gwamnati ta kan iya ɗaukar mataki kule ja'a a gidan kurkuku a kan ƙorafe-ƙorafen.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto hade dawanda Pinado Abdu ta rubuta mana a kan matsayin siyasa na ƙasar a kan al'amuran tattalin arziki.

Mawallafi: Thomas Mösch/ Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu