1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cikas a yaki da Ebola

October 6, 2014

Rashin kyawun yanayi da kuma isassun kayan aiki na dakile kokarin da ake yi na yakar cutar Ebola a yammacin Afirka.

https://p.dw.com/p/1DRBv
Hoto: Reuters/Christopher Black/WHO

Rashin kayan aiki da ruwan sama mai karfi sun kawo cikas a ayyukan da dakarun Amirka suke yi na taimakawa wajen yakar cutar Ebola a yankin yammacin Afirka. Sai dai a yanzu sojojin sun ce sun shirya tsaf wajen samar da tantuna da kuma asibitocin wucin gadi a Laberiya domin yakar wannan cuta.

Daya daga cikin sojojin Amirkan Laftanar Kanar Jason Brown ne ya shaida wa manema labarai hakan a Monrovia babban birnin kasar ta Laberiya, inda ya ce suna sa ran fara aikin samar da asibitocin da za su kula da ma'aikatan lafiyar da suka kamu da cutar Ebola a Litinin din nan. Cutar dai ta fi daukar rayuka a Laberiya, kasar da har kawo yanzu take fuskantar karancin gadajen kwantar da masu wannan cuta da kuma kayan aiki.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo