1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cimma burin wanzuwar da zaman lafiya a duniya

September 24, 2010

Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya buƙaci ƙarin tallafi da haɗin guiwa, wajen cimma burinsa na wanzar da zaman lafiya

https://p.dw.com/p/PM3m
Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-moon na jawabi da kwamitin sulhun MajalisarHoto: UN-Photo

Kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce zai buƙaci ƙarin tallafi da haɗin guiwa, wajen cimma shirin Majalisar Ɗinkin Ɗuniya na wanzar da zaman lafiya. A Wani taro da ke gudana daura da zauren babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya, hukumar ta ce dakarun ta guda 15 waɗanda suka haɗa da sojoji da farar hula dubu 122, na buƙatar tallafin da zai tabbatar da ce wa sun gudanar da aikin su yadda ya kamata, musamman wajen shawo kan fashi da ta'addancin da ake amfani da makamai masu hatsarin gaske.

Wen Jiabao Premiyan China wanda ƙasar sa take da kimanin ma'aikata dubu 14 a majalisar, ya ce ya zama wajibi a mai da hankali wajen inganta fannin shiga tsakani ta sulhu da kuma sauran harkokin kauce wa rikice-rikice tsakanin ƙasashe.

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Mrs Hillary Clinton ta ce sau da yawa rayukan dakaru kiyaye zaman lafiya kan fada cikin haɗari saboda  ƙarancin kayayyakin aiki da likitoci, da kuma jami'an 'yan sanda - masu bayar da horo.

Mawallafi: Pinaɗo Abdu

Edita: Umaru Aliyu