1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin hanci na yaɗuwa a Najeriya

December 10, 2013

Shugaban majalisar wakilan Aminu Waziri Tambuwal shi ne ya zargi shugaban ƙasar da gazawa wajen magance matsalar cin hanci a ƙasar.

https://p.dw.com/p/1AWTS
Symbolbild Geldgeschenk
Hoto: picture-alliance/dpa

Ba kasafai dai ya kan kai ga tsoma baki a cikin harkokin siyasar ƙasar ta Najeriya, to sai dai kuma maganganun sa kan yi ƙarfi da tasirin tada hankali ga shugabannin ƙasar. Kama daga gaza hukuntar da masu laifin sace rarar man fetur ɗin Tarrayar Najeriya, ya zuwa ɗaure gindi ga jami'an gwamnatin da ake zargi da sama da faɗi a cikin harkoki na mulkin ƙasar dai, Aminu Waziri Tambuwal bai yi wata-wata ba wajen zama ya bayyana jeri na laifukan da yake ganin sun kauce hanya a ƙoƙarin na kawo ƙarshen fata da ɓuri na ganin bayan annobar da ta yi ƙamari a Najeriyar.Sabon zargin da ke zaman na baya-baya dai na zaman mafi girma a ɓangaren wani jami'in gwamnatin ƙasar a dai-dai lokacin da fagen siyasar Tarayar Najeriya ke ƙara tsamari da ɗaukar hankali a yanzu haka.

Rashin yin hukunci na ƙara janyo cin hanci a Najeriyar

Abun kuma da ke ƙara tada hankali a ɓangaren mahukuntan da a baya ke cewar sun kai ga tabbatar da nasarar ɗiga ɗanbar ganin bayan annobar tare da ƙara inganta ginshiƙai na hukumomin yaƙar hancin cikin ƙasar.Hon Ahmed Idris dai na zaman ɗan kwamitin yaƙi da cin hanci a majalisar wakilan ƙasar kuma a faɗarsa abun da mahukuntan ƙasar ke faɗa bai yi kama da abun da 'yan ƙasar ke gani cikin ƙasa ba. Kauda ido ga batun cin hancin da nufin biyan buƙata ta siyasa ko kuma ƙoƙari na ƙazafi ga abokai na adawa dai, rahoton ƙungiyar Transparency International mai yaƙi da cin hanci da rashawa a matakin ƙasa da ƙasa dai ya ambato Tarrayar Najeriya a cikin ƙasashe 15 mafi ci hanci a duniya baki ɗaya.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Sai an tashi tsaye domin shawo kan matsalar ta cin hanci

Abun kuma da mahukuntan ke yi wa kallon na ci gaba ga ƙasar da a baya ta sha cire tutar farko ko ta biyu ga batun cin hancin a tsakanin 'yan uwanta ƙasashen duniya. Ƙasar ta Najeriya dai na da aƙalla hukumomi biyu masu ƙarfi ga batun yaƙin da tun bayan sake dawowar demokraɗiyyar ƙasar ke gaba ke baya.To sai dai kuma a faɗar Auwal Musa Rafsanjani da ke zaman ɗaya a cikin jami'an ƙungiyar Transparency international reshen Najeriya mai yaƙi da cin hanci matsalar cikin ƙasar na kama da yaudara a cikin yaƙin ba wai gazawa ta hukumomin wajen tabbatar da kawo ƙarshen annobar ba.Abun jira a gani dai na zaman mafita ga ƙoƙarin kawo ƙarshen annobar da ake danganta wa da zaman dalilin koma bayar ƙasar a cikin 'yan uwanta ƙasashen duniya.

1. Mai in Nigeria
Hoto: DW

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Abdourahamane Hassane

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani