1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin hanci ya tafi da kujerar shugabar kasar Mauritius

Mohammad Nasiru Awal
March 16, 2018

Wata jarida a Jamus ta ce 'yan ta'adda ba su da iyaka, ganin yadda aka yi garkuwa da 'yan matan makarantar Dapchi a Najeriya, da kuma yadda a ke zafafa hare-hare a babban birnin Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/2uShh
Deutschland Ameenah Gurib-Fakim in Dresden
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Kahnert

Jaridar Neue Zürcher Zeitung wanda ta leka kasar Mauritius, tana mai cewa shugabar kasar Ameenah Gurib-Fakim ta yi murabus sakamakon wata badakala ta rashawa. Jaridar ta ce a kasar ta Mauritius da ke a tekun Indiya ta kasance wani tsibiri da masu yawon shakatawa ke sha'awar zuwa, kasa ce da ke da shugabanci mafi kyau a nahiyar Afirka. A farkon mako ta yi bikin cika shekaru 50 da samun 'yancin kai daga kasar Birtaniya.

Sai dai batun murabus din shugabar mai shekaru58 da ke zama mace daya tilo da saura a kan mukamin shugabancin Afirka, ya dauki hankali. Ita dai Shugaba Ameenah Gurib-Fakim ta yi amfani ne da wani katin cin bashi wato Credit Card da wata kungiyar agaji ta ba ta don yin tafiye-tafiye a madadin kungiyar, amma sai ta yi amfani da katin wajen sayen kayan ado na kashin kanta da suka kai Euro dubu 25 a birnin London. Ko da yake ta ce ba ta aikata ba daidai ba, ta kuma biya kudin daga baya, amma biyan kudin kanshi na nufin amsa laifin zargin da ake mata, inji jaridar.

Nigeria Dapchi Schülerinnen nach Boko-Haram-Angriff auf Schule vermisst
Ministan labaran Najeriya, Alh. Lai Mohammed yayin ziyarar DapchiHoto: Reuters/O. Lanre

'Yan ta'adda da ba su da iyaka, inji jaridar Die Tageszeitung. Ta ce a Najeriya 'yan ta'adda sun yi garkuwa da 'yan mata 'yan makarantar sakadandare daga garin Dapchi da ke jihar Yobe. A kasar Burkina Faso wasu 'yan ta'adda ne suka kai hare-hare a tsakiyar babban birnin kasar. Hakan na nuni da yadda 'yan tarzoma masu daukar makami suka addabi wasu yankunan kasashen yammacin Afirka. Jaridar ta ce tun bayan juyin mulkin shekarar 2014, Burkina Faso ta yi rauni, inda a arewacin kasar kungiyoyin Jihadi suka samu gindin zama sannan wasu sun tsallako daga Mali, wadda ita kanta ma ke fama da tashe-tashen hankula na masu tada kayar baya da sunan addini. Yanzu haka ma wasu kungiyoyin 'yan tawaye ne suka kunno kai. Jaridar ta kara da cewa ko da yake ba bu sahihan bayanai dangane da girman kungiyoyi masu daukar makami a yammacin Afirka, duk da rashin yawan membobinsu suna da karfi suna kuma iya canja dubarun yaki, yayin da sojoji ke tangal-tangal, musamman ma dai a Najeriya.

DW - eco@africa: Plastikmüllverarbeitung zu synthetischem Öl
Wasu mata na tsintar leda a KenyaHoto: DW

Kenya ta daura damarar yaki da sharar leda a cewar jaridar Neue Zürcher Zeitung. Jaridar ta ce watanni shida ke nan da aka haramta amfani da jakar leda a Kenya, matakin da kasar ta dauka shi ne mafi tsanani a fadin duniya. Duk wanda aka kama da laifi za a ci shi tarar kudi mai yawa ko kuma a yi masa daurin shekaru hudu a kurkuku. Jaridar ta kara da cewa haramcin ba matsala ba ce ga manyan kantuna domin tuni sun maye gurbin jakar ledar da ta takarda ko kwalli, amma ga kananan masu saye da sayarwa a bakin hanya, haramci ya zame musu babban abin damuwa, domin sau da yawa farashin sabbin jakunan zuba kayan ya fi farashin ainihin kayan da suke sayarwa.