1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hillary Clinton ta samu wakilan da take bukata

Suleiman BabayoJune 7, 2016

Rahotanni daga Amirka na nuni da cewa Hillary Clinton ta samu wakilan da take bukata domin takara ga jam'iyyar Democrat ta Amirka a babban zaben kasar na watan Nuwamba mai zuwa.

https://p.dw.com/p/1J1jj
USA Hillary Clinton Los Angeles
Hoto: pictue-alliance/epa/P. Buck

Wani rahoton kamfanin dillancin labaran AP, ya nunar da cewa Hillary Clinton ta samu wakilan da take bukata, da suka hadar da mambobin jam'iyya da masu zaben bisa radin-kai 2383. Sai dai har yanzu tana fuskantar fafatawa daga Bernie Sanders wanda ke ci gaba da kafewa, yayin da a wannan Talata wasu jihohi za su kada kuri'a kan zaben na fitar da gwani na jam'iyyar ta Democrat.

Amma tana kara fitowa fili cewa Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrat za ta fafata da Donald Trump wanda tuni ya samu wakilan da yake bukata, wanda zai bashi damar yin takara ga ja'iyyar Republican a zaben shugaban kasar ta Amirka, domin samun wanda zai maye gurbin Shugaba Barack Obama wanda wa'adin mulkinsa na shekaru takwas ya kawo karshe.