1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cocin Katolika na shiga tsakani a Kwango

December 22, 2016

Cocin roman katolika da ke shiga tsakanin a rikicin da ake yi a Jamhuriyar demokaradiyyar Kwango ya yi gargadin cewar ya zama waji a samu sulhu kafin nan da bukukuwan Sallah Krismeti.

https://p.dw.com/p/2UhjR
Kongo Kinshasa CENCO Bischöfe, Fidele Nsielele & Marcel Utembi & Fridolin Ambongo
Hoto: Reuters/T. Mukoya

Cocin wacce tun da farko ta dakatar da shiga tsakanin saboda rashin cimma matsa da ba a yi ba tsakann 'yan siyasar, ta ce wannan jiko shi ne yunkurinta na karshe idan har ba a samu daidaituwa ba.Donatien Nshole na daya daga ciki jami'an Cocin da ke shiga tsakanin:''Yakamata 'yan siyasar su samu mafita kafin a kai ga yin da na sanni,akwai hanyoyi da dama da za mu ba da sharwari a bi domin warware takkadamar.

A shekaru gomai na baya-bayan nan Cocin na Catholika a Kwango ya taka muhimmiyar rawa wajen sassanta rikicin siyasar kasar tun bayan  da Laurent Desire Kabila mahaifin Joseph Kabila ya kifar da gwamnatin Mubutu Sese Seko a shekara ta 1997.