1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

David Cameron ya samu nasarar yin tazarce a Birtaniya

Mohammed Sani Dauda/LMJ May 8, 2015

Sakamakon zaben da aka yi a Birtaniya ya tabbatar da cewa jam'iyyar Conservative ta Firaminista David Cameron ta samu nasarar yin tazarce.

https://p.dw.com/p/1FMwm
Firaministan Birtaniya David Cameron ya yi tazarce
Firaministan Birtaniya David Cameron ya yi tazarceHoto: Getty Images/AFP/L. Neal

Jam'iyyar ta Conservative dai da ke da ra'ayin 'yan mazan jiya ta samu nasarar lashe kujeru mafiya rinjaye ta yadda hakan ya ba ta damar sake kafa gwamnati ba tare da kafa gwamnatin haadaka ba. Tunda farko a lokacin da yake cinye kujerar mazabarsa, Firaminista David Cameron da ya samu nasarar komawa kan karagar mulki a karo na biyu cewa ya yi matakan da suka dauki tashon shekaru biyar suna dauka wanda ke da matukar wahalarwa su ne suka taimaka masa wajen sake lashe zaben.

Jagoran babbar jam'iyyar adawa ta Labour Ed Miliband
Jagoran babbar jam'iyyar adawa ta Labour Ed MilibandHoto: Getty Images/M. Lewis

Gagarumin kaye ga Labour

Babbar jam'iyyar adawa ta Labour ta sha kaye da gagarumin rinjayen a wannan zabe, duk kuwa da cewa har kawo ranar zaben suna kunnen doki ne da jam'iyya mai mulki ta Conservative. Da yake matashiya bisa kayen da jam'iyyarsa ta sha, shugaban jam'iyyar ta Labour Ed Miliband cewa ya yi:

"Wannan dare ne mai wahala kuma maras kyau ga jam'iyyar Labour. Mun gaza cimma burimmu na taka rawar gani a wannan zabe".

Scottish National Party ta yi rawar gani

Ita kuwa jam'iyyar kishin kasa ta Scotland wato Scottish National Party ta lashe baki dayan kujerun fadar mulki ta Westminster da ke London, inda shugabanta da ya jagoranci kuri'ar raba gardama ta neman ballewar yankin daga Birtaniyan Alex Salmon ya samu nasarar lashe kujerar majalisar, wanda hakan ke nuni da cewa jam'iyyar ta yi rawar gani a zaben. Jam'iyyar Liberal Democrats kuwa da ke cikin gwamnatin hadin gwiwa da Conservative tsawon shekaru biyar al'amarin ya kwabe mata domin kuwa ta yi asarar kujerun majalisar 46 inda suka tashi da kujeru takwas kacal daga cikin kujeru 54 da suke da su gabanin zaben. Jam'iyyar da ke adawa da kwararar baki zuwa Birtaniya kuwa ta UKIP ta samu nasarar lashe kaso 13 cikin 100 ne na kuri'un da aka kada yayin zaben.

Scottish National Party na murnar taka rawar gani a zaben.
Scottish National Party na murnar taka rawar gani a zaben.Hoto: AP