1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen da ke gaban Olaf Scholz

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 9, 2021

Babban kalubalen da sabuwar gwamnatin Jamus za ta fuskanta shi ne, yaki da annobar Covid-19 da ke neman zame wa kasar karfen kafa.

https://p.dw.com/p/442ec
Deutschland neue Bundesregierung
Sabuwar gwamnatin hadaka ta Jamus, karkashin jagorancin Olaf ScholzHoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

A cewar sabon shugabangwamnatin ta Jamus Olaf Scholz ya zama awajibi Berlin ta yi wani tanadi, domin tunkarar annobar coronavirus din da take ci gaba da yin dauki dai-dai a kasar. A jawabinsa yayin da yake mika ragamar ma'aikatar kudi ga Christian Lindner sabon minista kudin Jamus kana shugaban jam'iyyar Free Democrats (FDP) ta hadaka a Jamus din, Scholz ya nunar da cewa ma'aikatar kudi na da gagarumar rawar takwa a gwamnatin hadakar ta jam'iyyu uku. 

Ana jiran ganin kamun ludayin sabuwar gwamnatin ta Jamus a fannin diflomasiyya, a cikin yanayin rudanin siyasa tsakanin kasashen yamma da Rasha da Chaina. Ita dai sabuwar ministar harkokin waje Annalena Baerbock ta yi alkawarin nesanta kanta daga manufofin waje na gwamnatin da ta gabata dangane da rikicin da ya shafi Rasha, sakamakon yadda birnin Moscow ke jibge sojoji a kan iyakokin kasar Ukraine, lamarin da ke kara nuna fargabar kai hari.

Sai dai a wani sakon taya murna ga sabuwan shugabar gwamnatin Jamus, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi fatan kulla alaka mai kyau da Olaf Scholz. 'Yan majalisar dokoki na Jamus 395 ne suka zabi Olaf Scholz a matsayin sabon shugaban gwamnati, yayin da 303 suka ki amincewa da shi guda shida kuma suka yi rowar kuri'unsu. Wannan matakin ya ba shi damar zama shugaban gwamnatin Jamus na tara bayan yakin duniya, wanda kuma shugaban kasar Frank-Walter Steinmeier ya rantsar da shi da kuma ministacinsa 16.