1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rufe filayen jiragen saman Najeriya

Uwais Abubakar Idris ZU
March 21, 2020

Gwamnatin Najeriya ta sanar a yammacin wannan Asabar cewa ta rufe manyan filayen jiragen samanta na Abuja babban birnin kasar da na Legas wanda ke zama cibiyar kasuwancin kasar.

https://p.dw.com/p/3Zqlc
Nigeria Abuja Flughafen Eröffnung
Hoto: picture-alliance/AP/S. Aghaeze

Hukumomi sun dauki matakin ne biyo bayan samun karuwar masu dauke da cutar Coronavirus wadda kawo yammacin ranar Asabar mutane 22 ke dauke da ita a kasar. 

Matakin rufe filayen jiragen saman na Legas da Abujan wadanda sune kadai da gwamnatin ba ta rufe wa jiragen kasashen duniya ba, zai fara aiki daga ranar Litinin 23 ga watan nan na Maris. 

Nigeria Nnamdi Azikiwe International Airport in Abuja
Jama'a a filin jirgin saman Abuja na Najeriya a wani hoto da aka dauka a 2013Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

 

Henrietta Yakubu ita ce mai magana da yawun hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya. Ta kuma shaida wa wakilinmu na Abuja Uwais Abubakar Idris cewa karuwar cutar Coronavirus ce ta sa aka dauki wannan mataki.

Hukumomi dai sun ce za a dauki tsawon wata guda ana hana jiragen sama daga kasashen waje zuwa Najeriyar. Sai dai za a iya bude kofa idan aka samu bukata ta gaggawa.