1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COVID-19: Najeriya na son tallafin Chaina

April 6, 2020

A yayin da Tarayyar Najeriya take ci gaba da kokarin tunkarar annobar COVID-19, takaddama ta barke tsakanin gwamnati da ta ce tana shirin karbar wasu likitoci daga Chaina da kuma likitocin kasar da ke fadin bai dace ba.

https://p.dw.com/p/3aWvl
Nigeria Präsident Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari na NajeriyaHoto: picture alliance/AP Photo/S. Alamba

Akalla kwararrun likitoci har 18 ne dai ma'aikatar lafiya taTarayyar Najeriyar ta ce tana shirin karbar bakunci daga Chainan, da nufin hada hannu a cikin yaki da COVID-19 da ke ta nuna alamu na karuwa cikin kasar ya zuwa yanzu. To sai dai kuma kungiyar likitocin Najeriyar ta NMA ta ce kasar na da kwararrun likitoci kayan aiki kawai suke da bukata domin tunkarar annobar, maimakon likitoci na waje.
Duk da gazawar kayan aikin da ma rashin kyawun yanayin aikin dai, NMA ta ce likitoci da ma ragowar jami'ai na lafiya na nuna kwarewa a wajen wannan yakin, kuma babu bukatar wani taimakon da a cewar Francis Adedayo da ke zaman shugaban kungiyar likitocin, ka iya zama mai hatsari ga kasar:

Symbolbild - Ebola
Likitocin Najeriya na bukatar kayan aikiHoto: picture-alliance/AP/S. Alamba

Tallafi daga nesa

"Babu wani abu sabo da 'yan Chaina za su iya bamu, in ma akwai mun sha nanatawa cewar fasaha ta zamani ta saukaka lamura, ba sai sun hada fuska da marasa lafiyarmu ba, ba sa bukatar zuwa kasarmu, ba sa bukatar killace kai na tsawon makonni biyu kamar yadda dokarmu ta tanada. Muna iya nazari ta kafar Skype ko kuma ragowar kafafen sadarwa na zamani, sannan kuma mu dora daga nan. Ba dole ba ne sai sun kasance a nan,   sannan kuma abu ne da ya shafi dokokin aikin ya kuma shafi tsarin tsaron kasarmu, dole ne kuma mu kare yankinmu."

China Hilfe Pakistan
Likitocin Chaina na zuwa wasu kasashe domin kai daukiHoto: Getty Images

Kokarin tsare gida ko kuma agaji na dolen-dole, ra'ayi ya banbanta ko a tsakani na kwararrun likitocin kasar. Farfesa  Abdusallam Nasidi na zaman tsohon shugaban cibiyar kula da cututtuka ta kasar mutumin kuma da ya jagoranci yakin kasar da Ebola, a tunaninsa akwai bukata ta taimakon da ma kila komawa cikin gida da nufin sake zakulo kwararrun da suka taka rawa wajen kai karshen annobar ta Ebola.

Hada hannu domin yakar cutar

Duk da cewar dai Najeriyar na nuna alamun nasara tare da samun warkewar da ta kai kusan kaso 14 cikin dari  na masu dauke da cutar da kuma asara ta rayukan da ba ta wuci kaso biyu a cikin dari ba dai, sabuwar dabara ta duniya a fadar Dr Ado Mohammed da ke bai wa kasashen D8 shawara a harkar lafiyar, na zaman hada hannu da kafada cikin sabon yakin. Ya zuwa yanzu dai, mutane 232 ne a fadar cibiyar kula da cutakan Najeriyar ta ce sun kamu da wannan cuta cikin kasar, a yayin kuma da 33 suka warke. To sai dai kuma kasar ta shiga sabon mako kila  ma makon karshe na a zauna a gida da asarar mutane  biyar sakamakon annobar ta COVID-19.