1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Covid-19 ta haddasa rashin aiki a duniya

Abdullahi Tanko Bala GAT
May 28, 2020

Kungiyar Kwadago ta Duniya ILO ta yi kiyasin cewa an yi hasarar kusan kashi 11 cikin dari na sana'o'in aiki a duniya baki daya saboda annobar corona a zango na biyu na wannan shekarar.

https://p.dw.com/p/3cv4p
Thailand Arbeit Migranten Arbeiter Meeresfrüchte
Hoto: International Labour Organization

Kungiyar Kwadago ta Duniya ILO ta yi kiyasin cewa an yi hasarar kusan kashi 11 cikin dari na sana'o'in aiki a duniya baki daya saboda annobar corona a zango na biyu na wannan shekarar. Wannan adadi ya kai kwatankwaci guraben ayyuka miliyan 305 a cewar rahoton baya bayan nan da kungiyar ta ILO ta gabatar kan annobar COVID 19 a jiya Laraba a birnin Geneva. 

Kungiyar Kwadagon ta Duniya ILO ta ce kamar yadda alkalumma suka nuna, matasa 'yan tsakanin shekaru 15 zuwa 24 ne musamman lamarin ya fi shafa. Kuma tun kafin annobar ba abu ne mai sauki ba ga matasa wurin samun aiki. Kungiyar ta ce rashin aiki a tsakanin wannan rukuni na mutane ya wuce mizani, inda yawanci suke ayyuka na bayan fage da ake biyansu 'yan kudin da ba su taka kara sun karya ba a cewar Guy Ryder babban darakta a Kungiyar Kwadago ta Duniya:

"Matasa ko shaka babu ana iya cewa suna bakin daga ne. Su lamarin ya fi shafa cikin gaggawa da kuma matukar illa fiye da sauran jama'a. Daga cikin matasa da suke aiki a farkon barkewar annobar daya a cikin mutum shidda a yanzu ba sa aiki".

Costa Rica Bananenplantagenarbeiter Gewerkschaftsarbeit
Hoto: AP

Kungiyar Kwadagon ta Duniya na kallon matasan da wannan annoba ta shafa ta fuskoki uku. Na farko sun rasa ayyukansu ga babu ilmi sannan horon sanin makamar aiki da suke samu baya dorewa yayin da a waje guda wadanda suka gama makaranta a yanzu suka shiga fafutukar neman aiki. Binciken kungiyar kwadagon ya nuna cewa idan mutane ba za su iya yin aiki na tsawon lokaci a fannin da suka kware a rayuwarsu ba, to kuwa akwai tasiri da hakan zai haifar na tsawon shekaru da dama. Ryder ya ce hakan na nufin cewa ba za su iya cimma buri ba ko samun wani ci-gaba a bigire na kwararru, hasali ma, ana iya cewa akwai hadarin kulle ko zaman gida ga wani rukuni na matasa manyan gobe a nan gaba:

"Kari a kan halin komabaya da mata suka samun kansu a ciki gabanin annobar corona, shi ne cewa mata, musamman 'yan mata suna da yawa a wasu sassa da annobar ta yi wa katutu. fannin abinci da matsuguni da sha'anin otel-otel da bangaren 'yan sari masu sayen dai dai da kuma manyan diloli. A saboda haka a takaice suna tsakiyar wuri mafi hadari"

ILO-Konferenz 2004
Hoto: picture-alliance/ dpa

Domin rage wadannan illoli da kuma kare daukacin mayan gobe daga tawaya ko komabaya, kungiyar kwadagon ta duniya ta yi kira ga gwamnatoci su dauki managartan matakai cikin gaggawa. Kungiyar ta ce abin tambaya shi ne wane ne zai biya dukkan wannan hasara a yayin da gwamnatoci ke kukan dumbin bashi da ya yi musu katutu? A halin da ake ciki dai Kungiyar Tarayyar Turai na tattauna gidauniyar tallafi na kimanin Euro biliyan 750. Sai dai kuma kasashe da dama musamman masu raunin tattalin arziki na daga cikin kasashen da cutar corona ke yaduwa da gaggawa a cikinsu kamar yankin kudancin Amirka.