1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Ebola ta hallaka jami'in Majalisar Dinkin Duniya

October 14, 2014

Wani jami'i da ya kamu da cutar Ebola a Laberiya da aka kawo shi Jamus domin samun magani ya hallaka

https://p.dw.com/p/1DVRB
Leipzig St. Georg Krankenhaus Sachsen Deutschland Ebola Patient
Hoto: picture-alliance/dpa/Hendrik Schmidt

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutanen da suka tsira daga cutar Ebola, kuma aka tabbatar suna kariya daga sake kamuwa da cutar za su gudanar da taro a kasar Saliyo cikin wannan mako, domin guba hanyoyin da za su taimaka wajen dakile cutar.

Taron na gobe Laraba da jibi Alhamis, a yankin kudu maso gabashin Saliyo, zai samu halarcin mutane 35 da suka tsira daga cutar, domin ganin hanyoyin da za su taimako cikin yunkurin kawo karshen cutar ta Ebola.

A wani labarin wani ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya ya rasu sakamakon kamuwa da cutar Ebola, wanda aka kawo nan Jamus domin jinya. jami'in dan shekaru 56 da haihuwa, ya kamu da cutar a kasar Laberiya. Jami'an kiwon lafiya sun ce jami'in majalisar likita ne dan kasar Sudan, wanda aka kai shi asibitin da ke garin Leipzig na nan Jamus a makon jiya. Ya zuwa cutar Ebola ta kama fiye da mutane 8000, kuma tuni ta hallaka kimanin 4000 daga ciki.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu