1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar murar tsuntsaye naci gaba da ta´adi

Ibrahim SaniNovember 8, 2005

Masana kiwon lafiya naci gaba da taron kolin samo bakin zaren dakile yaduwar cutar murar tsuntsaye a wasu kasashe na duniya

https://p.dw.com/p/BvUU
Hoto: AP

Ya zuwa yanzu dai babban abin da yafi daukar hankali shine na rasuwar wani mutum daya dake kasar Vietnam sakamakon kamuwa da yayi da cutar murar tsuntsayen.

Bugu da kari awowi kadan bayan faruwar hakan sai ga wani sabon labari kuma daga kasar Indonesia dake nuni da cewa yarinyar data rasa ranta a kasar Jiya,nada nasaba da kamuwa da tayi da wannan cuta ta murar tsuntsayen.

Wannan cuta dai ya zuwa yanzu bayanai sun shaidar da cewa tayi barna mai yawan gaske na asarar tsuntsaye miliyoyin gaske mutane kuma da suka rasa rayukan su sakamakon cin naman kajin dake daukar da wannan cuta.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa wannan cuta tafi tsanan ta ne a kasashen Asia da gabashin nahiyar Turai. Kuma a cewar bayanai da alama wannan cuta ka iya bazama izuwa kasashen gabas ta tsakiya da kuma nahiyar Africa, matukar ba´ayi hankali ba.

Bisa kuwa asarar rai na 42 da akayi a kasar ta Vietnam a sabili da wannan cuta ta murar tsuntsayen, kwamishinan lafiya na kungiyyar tarayyar Turai ya bukaci kasashen duniya dasu tashi tsaye haikan wajen daukar matakan gaggawa na shawo kann wannan matsala tun kafin ta gagari kundila.

wannan al´amari ya haifar masana kiwon lafiya dake ci gaba da taron kwanaki uku a birnin Geneva ci gaba da tunanin mataki na gaggawa daya kamata a dauka don kare ci gaba da afkuwar wannan al´amari.

A cewar mahalarta wannan taro na Geneva, bayan an samu damar shawo kann wannan cuta ta murar tsuntsayen, abu guda kuma da za a bawa muhimnanci shine na tallafawa manoma da sukayi mummunan asara sakamakon kamuwa da tsuntsayen su suka yi da wannan cuta.

A yayin da kuwa ake cikin wannan hali hukumar kula da harkokin noma ta mdd cewa tayi cutar muruar tsuntsaye dake addabar wasu kasashe na duniya abune da za a iya shawo kann sa gaba daya daga doron kasa.

Ya zuwa yanzu bayanai sun yi nuni da cewa kamfanin hada magungunan nan na Swiss yace yana nan yana ci gaba da tattaunawa da wasu kamfaninnika na hada magunguna a kokarin da suke na hada hannu da hannaye guri guda don samar da maganin nan na yaki da wannan cuta mai suna Tami Flu a turance, wanda ya zuwa ya kasance kwaya daya tilo daya fi ko wane magani yakar wannan cuta.

A kuwa ta bakin babban daraktan hukumar lafiya ta duniya wato Lee Jong Wook, cewa yayi yaduwar wannan cuta nada asaline da tsuntsaye masu balaguro daga wuri izuwa wani wurin wanda ta hakan ne da yawa daga cikin tsuntsayen gida suka kamu da ita.

Lee Wook ya dai fadi hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabin sa a gaban taron kolin masana kiwon lafiyar a birnin na Geneva.

Bugu da kari hukumasr ta lafiya ta kuma bukaci kasar sin da sauran kasashen dake fama da wannan annoba dasu rinka musayar bayanai na irin yadda cutar take da kuma matakan da ake dauka na kariya a tsakanin kasashen duniya da kuma hukumomi na lafiya don hana ci gaba da yaduwar ta a duniya.

A daya bangaren kuma bankin duniya yace barkewar wannan cuta da kasancewar ta tsawon shekara daya ba tare da an shawo kann ta ba a yanzu haka tayi sanadiyyar gurguncewar tattalin arzikin duniya da dalar Amurka biliyan dari takwas.

Bisa kuwa wannan abu, bankin na duniya yace zai kaddamar da asusun neman tallafi na dalar Amurka biliyan daya a lokacin wannan taro da ake a birnin na Geneva don yin amfani dasu wajen tsaurara binciken samo babbar hanyar maganin wannan annoba.