1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar sankarau na kashe rayuka a Najeriya

March 28, 2017

Mutane da dama ne suka mutu a sakamakon cutar sankarau a Jihohin Kebbi da Zamfara da Sokoto da ke a arewa maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/2aApR
Nigeria Falumata Muhammed trotzt Boko Haram
Hoto: DW/A. Kriesch

Cutar Dan sankarau na kokarin mamaye yankin arewa maso yammacin Najeriya Inda ake kara samun yawaitar mutane masu mutuwa kusan kowace rana a Jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara. Mafi yawancin alkalumman gwamnati na bayyana yawan wadanda suka mutu a asibiti  a yayin da wasu ke mutuwa a gidajensu saboda rashin abin hannu da za su dauki dawainiyar kansu a asibiti.Yanzu haka dai hukumomin lafiya na daukar matakai na shawo kan matsalar ta hanyar riga kafi da ba da magani da kuma yekuwar wayar da kai a kan kaucewa kwanciya a cikin dakuna saboda tsananin zafi.

A shekarun baya ma daI haka aka yi ta fama da irin wannan annoba ta cutar dan sankarau a cikin jihohin na arewacin Najeriya.