1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi mai kirkira a Najeriya

Al-Amin Suleiman Muhammad/LMJAugust 3, 2016

Malam Ukasha wani bawan Allah ne mai sana’ar walda da ke da basirar kirkirar kayayyakin gyara na ababan hawa wanda a ke kira da "Spare Parts" a Turancin Ingilishi, wadanda kuma ke da wuyar samu.

https://p.dw.com/p/1Jb9s
Sana'ar kanikanci da samar da bangarorin ababen hawa
Sana'ar kanikanci da samar da bangarorin ababen hawaHoto: Simone Schlindwein

Shi dai Malam Ukasha wanda asalin sana'arsa walda da kera kofofi, yanzu ya shahara wajen kera wasu bangarorin ababan hawa da kuma wasu na'urori na amfanin gida kamar injin yin taliya da kuma na markade da makamantan su wanda masu kanan sana'o'i ke amfani da su. Akwai tsofaffin motoci ko wasu na'ururi da ake wahalar samun kayayyakin gyara su wani lokaci ma akan hakura da ababen hawan saboda karancin kayan gyara da ake kira da "Spare parts" a Turancin Ingilishi. Bisa wannan ne Malam Ukasha ya samu fasahar kera wasu daga cikin irin wadannan kayayyakin gyara da kuma ake amfani da su na tswon lokaci ba tare da sun baci ba kuma yana hadawa da fasaha ta zamani. baya ga wadannan abbuwan da yake kerawa a masana'antar sa, Ukasha yana kuma kera injinan domin amfanin manoma kamar na chasar shinkafa da gyada da na'urar bare masara da makamantan su. Haka kuma Malam Uksha na da wani shiri na horar da matasa wannan sana'a tasa, inda bayan kammala horo yana bai wa matasan kayan aiki da jari don dogaro da kai. Ya zuwa yanzu kusan matasa 200 ne suka koyi sana'a daga wannan shiri nasa inda kuma yake ci gaba da daukar wasu matasan domin rage rashin ayyuka da zaman banza tsakin matasa.