1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dage zaben Togo ya bar baya da kura

Mouhamadou Awal Balarabe/ PAWMarch 30, 2015

Wa'adin da aka diba na dage zaben, ka iya sabawa tanadin dokokin kasar domin duk wani jinkiri zai iya tasiri kan lokacin gabatar da sakamako.

https://p.dw.com/p/1Ezk3
Faure Gnassingbe
Hoto: AP

A Togo, dage zaben shugaban kasa da aka yi daga 15 zuwa 25 ga watan Afrilu mai zuwa a bar baya da kura saboda karar tsaye da zai iya yi wa kundin tsarin mulkin kasar. Shugaban kasar Ghana kana shagabn ECOWAS John Mahama ne ya bukaci karin kwanaki goma domin baiwa hukumar zabe damar magance kura-kuran dake tattare da rejistar masu kada kuri'a, lamarin da ya haifar da zazzafar mahawara a kasar ta Togo.

Tanadin kundin tsarin mulkin kasar

Bisa ga tanadin kundin tsarin mulkin kasar Togo dai, kafin uku ga watan Mayu mai zuwa ne ya kamata a sanar da sunan wanda ya lashe zaben shugaban kasa ko ma dai yaushe ne aka gudanar da shi, saboda haka, daga zaben da aka yi daga 15 zuwa 25 ga watan Afirlu zai iya yi karar tsaye ga dokokin kasar matukar dai aka fuskanci wata matsala wajen kidaya kuri'a ko kuma wani bangare ya shigar da kara. A dalilin haka ne Paul Amegakpo da ke zama shugaban wata kungiyar farar hula, kana kwararre a kan harkar zabe ya ke ganin cewa da sakel.

"A wannan wa'adi na kwanaki goma, dole ne a dibar wa hukumar zabe kwanaki biyu na bayyana sakamakon zabe, karin kwanaki biyar kuma na shigar da kararrakin zabe. Ita kuwa kotun tsarin mulki na da kwana daya tak na sauransu tare da bayyana sakamakon din-din-din. Muna ganin cewa wannan lokaci ya yi kadan. Dole ne ita kotun ta tsarin mulki ta bayyna ko shugaban kasa zai iya ci gaba da rikon kwarya bayan cikan wa'adinsa na mulki."

Ya zuwa yanzu dai kotun ta tsarin mulkin kasar ta Togo ba ta ce uffan ba. Amma kuma Jam'iyyar da ke mulki a Togo da kuma bangaren adawa sun yi maraba da matakin kwaskware jadawalin zabe da aka dauka. Ba don komai ba sai don amfani da tsukin kwanaki goman da aka kara da za su yi wajen tabbatar da cewar magoya bayansu su yi rejista.

Togo Wahlen
A shekara ta 2013 aka yi zabeHoto: Getty Images/AFP/Pius Utomi Ekpei

Korafin bangaren adawa

Da ma dai madugun 'yan adawan kasar ta Togo Jean-Pierre Fabre ya dade ya na korafin dangane da kitso da kawarkwata da ake da niyyan yi idan ba idan ba a sabonta rajistar masu kada kuri'a da ma dai dokokin da suka shafi tsarin gudanar da zaben ba. Saboda haka ne dai shugaba John Dramani Mahama na Ghana wanda yanzu haka yake shugabantar kungiyar, ECOWAS/CEDEAO ya shiga tsakanin bangarorin biyu.

Shawara daya tilo ya bayar wacce ba wata bace illa dai karin kwanaki goma don bawa kowa damar shiryawa caf, lamarin da gwamnati ba a yi wata-wata wajen amincewa da shi ba. Su ma dai wasu daga cikin 'yan kasar ta Togo ba a barsu a baya wajen tofa albarkacin bakinsu kan wannan dagen zaben shugaba kasar ba.

Westafrikanische Präsidenten fordern zivile Regierung in Burkina Faso 05.11.2014
ECOWAS ta sa baki dan ganin komai ya gudana cikin kwanciyar hankaliHoto: AFP/Getty Images/I. Sanogo

"Idan dai sun tabbatar da cewa wannan mataki zai bayar da damar inganta harkokin zabe a kasar nan, to wannan abin yin na'am da shi ne. Mu dai ba ma san abin da zai haifar da tashin hankali a lokacin zabe. Mun fi so a gudanar da shi cikin gaskiya da rikon amana."