1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun kotunan musulunci sun tsere daga Kismayo

January 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuVu

Rahotanni daga kasar Somalia sunce magoya bayan kotunan Islama sun tsere daga yanki na karshe da suke rike da shi na Jilib dake kusa da garin Kismayu.

Rahotannin sunce dakarun islaman sun nufi bakin iyaka kasar Kenya yayinda dakarun gwamnati da Habasha suka kutsa Kismayo.

A dai ranar alhamis ne dakarun kotunan musuluncin suka fice daga birnin Mogadishu bayanda dakarun kasar Habasha suka kai farmaki birnin.

A halinda ake ciki firaminista Ali Muhammad Gedi ya tabbatar da cewa yanzu haka Kismayo na hannun dakarun gwamnatin kasar ta Somalia.

Ministan yada labari na Somalia Ali Jama ya sanarda kanfanin dillancin labaru na Reuters cewa gwamnatin wucin gadi ta Somalia ta lashi takobin bin magoya bayan kotunan musulunci duk inda suka shiga.

Ali jama yace da zarar an gano inda suke dole ne abi bayansu don suna hade ne a cewarsa da mayakan kasashen ketare wadanda kasancewarasu a Somalia zai kawo illa ga tsaron kasar.