1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Kwango na samun galaba

November 3, 2013

Kungiyar 'yan tawayen M23 ta Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango ta ayyana tsagaita wuta.

https://p.dw.com/p/1AAyB
Hoto: picture alliance/AP Photo

Shugaban bangaren siyasa na kungiyar M23 ta 'yan tawayen Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango, ya aiyana tsagaita wuta, tare da neman mambobin kungiyar su ajiye makamai, domin tabbatar da shirin sasantawa da gwamnati.

Bertrand Bisimwa ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.

Dakarun gwamnatin kasar ta Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango sun sake kai wa 'yan tawayen M23 farmaki a tungarsu da ke gabashin wannan kasa. Wannan kuwa ya zo ne a dai-dai lokacin da taron sulhu tsakanin sassan biyu ke tafiyar hawainiya a birnin Kampala na Uganda.

Masu aiko da rahotannin sun nunar da cewa har ya zuwa wannan lokaci ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin sojojin na Kwango da kuma 'yan tawayen na kungiyar M23 kuma akwai alamun dakarun gwamnati na samun galaba. Tun ranar 25 ga watan Oktoba ne dakarun gwamnatin Kwango suka fara kai wa 'yan tawaye samame tare da kwace muhimman wurare da kuma garuruwa daga hannunsu.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh