1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Libiya da na Haftar na bata kashi

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
April 29, 2019

Gumurzu tsakanin dakarun Janar Haftar da sojojin gwamnatin Libiya a kusa da rijiyoyin mai na ci gaba da haddasa asarar dukiyoyi, yayin da 'yan kasar da dama ke kaurace wa matsugunansu.

https://p.dw.com/p/3HfCu
Lybien Truppen der libyschen Einheitsregierung starten Gegenoffensive
Hoto: Getty Images/AFP/M. Turkia

Sojojin da ke biyeyya ga madugun yakin Libiya Khalifa Haftar da masu goyon bayan gwamnatin Tiripoli sun yi wani gumurzu a wannan Litinin, a kusa da wasu rijiyoyin man fetur na Al-Sharara  mafi girma da ke kudancin kasar. Rijiyoyin na samar da danyen man fetur  akalla ganga dubu 315 a kowace rana daga cikin gangar danyen mai fiye da miliyan daya da kasar ta Libiya ke samarwa a rana.

Sai dai a lokacin da yake magana da manema labarai, kamfanin ya ce gumurzun da dakarun bangaroron biyu suka yi bai shafi ko guda daga cikin ma'aikatansa ba. Ya zuwa yanzu bata kashin da bangarorin ke yi a kasar sun halaka mutane 278 akalla tare da jikkata wasu fiye da dubu daya kana kuma akalla dubu 40 suka kaurace wa gidajensu in ji Hukumar Lafiya ta Duniya OMS.