1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dalibai a Hong Kong sun ki mika wuya

December 3, 2014

Joshua Wong shugaban daliban da suka shiga wannan zanga-zanga ya kira dalibai da su kara tattaruwa a wannan cibiya da suka mamaye don ci gaba da fafutuka.

https://p.dw.com/p/1DyVh
Hongkong Protest und Zusammenstöße 28.11.2014
Hoto: Reuters/Bobby Yip

Daruruwan masu zanga-zangar rajin ganin an kafa dimokradiya a Hong Kong sun bijirewa umarnin da aka basu na su kauracewa sansanonin da suka mamaye a cibiyar harkokin kasuwancin da ke a yankin Asiya bayan da shugabanninsu suka bukaci ganin hakan.

Da dama dai cikin wadannan masu zanga-zanga na ci gaba da tsayawa a tsakiyar wannan cibiyar hada-hadar kasuwanci kuma sun ce zasu ci gaba da fafutukar da suke na ganin an gudanar da sahihin zabe a wannan birni da ke karkashin mahukuntan kasar China.

Wanda ya kafa wannan fafutuka a jiya Talata ya bukaci magoya bayansa da su koma gida saboda fargabar ballewar rikici, bayan da Joshua Wong shugaban daliban ya kira dalibai da su kara tattaruwa a wannan cibiya da suka mamaya.

A cewar wasu daliban su tattara kayansu su koma gida ba tare da cimma wani abun azo a gani ba kan wannan fafutuka bai dace ba.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu