1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Akwai lauje cikin nadi a kisan mai rajin kare baki

Mouhamadou Awal Balarabe RGB
June 18, 2019

Bincike da ake gudanarwa kan kisan gilla da aka yi wa dan siyasa Walter Lübcke da ke rajin kare baki 'yan gudun hijra ya nunar da cewa kisa ne mai alaka da siyasa.

https://p.dw.com/p/3Kddb
Deutschland Trauerfeier für Walter Lübcke, Kasseler Regierungspräsident
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Pförtner

Dama wanda ake zargi da aikata danyen aiki ya taba kai farmaki a gidan da ake tsugunar da masu neman mafaka a shekarar 1993, lamarin da ke nuna tsatsauran ra'ayin siyasa da yake da shi. Alamu na dada fitowa fili cewa manufar siyasa ce ta sa aka kashe Walter Lübcke dan siyasa na gundumar Kassel da ke yankin tsakiyar Jamus. A yayin taron manaima labarai da ya gudanar a birnin Karlsruhe, ofishin babban mai shigar da kara na tarayya ya ce wanda ya tabka danyen aiki ya rugumi akidar tsaurin ra'ayin rikau na siyasa. Ita ma jaridar Zeit Online ta ce an kama Stephan E. tun ranar asabar domin zurfafa bincike, ya taba kai hari da wani abin fashewa a cibiyar da ake tsugunar da masu neman mafaka a jihar Hessen a shekarar 1993 a lokacin da yake da shekaru 20 da haihuwa, sai dai ba a samu asarar rayuka ba saboda bam din bai tashi ba, lamarin da ya sa aka  yanke wa Stephan E. hukuncin dauri na zaman kurkuku.

Deutschland Ermittlungen im Fall Lübcke
Kwanaki 16 da suka gabata aka halaka Lübcke mai shekaru 65 a gidansaHoto: picture-alliance/dpa/S. Pförtner

Binciken na dogaro a kan kalaman da ya taba furtawa a bainan jama'a, da kuma alakarsa da 'yan Nazi. Kotun na kokarin sanin ko ya hada kai da wasu abokan burmi wajen kisan da ake zarginsa da aikatawa. Stephan E. mai 'ya'ya biyu mamba ne na rashen jam'iyyar NPD ta 'yan Nazi a jihar Hessen. Kuma an taba yanke masa hukuncin watanni bakwai bisa fitinar da suka tayar a ranar daya ga watan Mayu na shekarar 2009 a Dortmund, tare da wasu masu akidar 'yan Nazi 400.

Marigayi Walter Lübcke, wanda tsohon babban jami'in gwamnati mai shekaru 65, an samu gawarsa ne kwanaki 16 da suka gabata a gidansa da ke kusa da birnin Kassel. Idan laifin kisan bisa dalili na siyasa ya tabbata, zai zama na farko irinsa a Jamus tun bayan hare-haren da masu tsatsauran ra'ayin suka kaddamar a shekarun 1970. Ko da shi ke a shekarar 1981, masu irin wannan akida sun kashe kwamishinan tattalin arzikin na yankin, wanda memba na jam'iyyar FDP da ke da rajin bunkasa harkokin cinikayya.

Yawancin jam'iyyun da ke da matsakaicin ra'ayin gurguzu sun yi kira da a yi zama na musamman a majalisar dokoki ta Bundestag a daidai lokacin da akidar kyamar baki ke ci gaba da samun karbuwa a zabuka dabam-dabam.Lübcke ya shiga kannun labarai ne sakamakon amincewa da ya yi da matakin da Shugaban gwamnati Angela Merkel ta dauka na bude kofofin Jamus ga 'yan gudun hijira a shekara ta 2015. ko da a  watan Oktoba na shekarar da ta gabata, lamarin da ya sanya tun a wannan lokaci aka yi barazanar kashe shi.