1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwar Siyasa a Israila

November 21, 2005
https://p.dw.com/p/BvK7

Yan majalisar dokokin Israila sun kada kuriá da gagarumar rinjaye domin amincewa kudirin rushe majalisar dokokin mai wakilai 120 wanda zai bada damar gudanar da sabon zabe a farkon shekara mai zuwa. Wannan matakin ya biyo bayan shawarar da jamíyar Labaour karkashin sabon shugaban ta Amir Peretz ta zartar ne inda ta janye daga gwamnatin hadin gwiwar. Ariel Sharon ya shafe tsawon watanni yana fafutukar dinke barakar da ta wanzu a gwamnatin sa, to amma shawarar da janyewar jamíyar ta Labour ta sanya ba shi da wani zabi. Sharon wanda a yanzu ya fice daga Jamíyar sa ta Likud ya sha alwashin kafa wata sabuwar jamíyar a nan gaba. Manazarta alámuran yau da kullum na baiyana cewa akawai alamun sabuwar jamíyar da sharon din zai kafa, zata sami goyon baya a zabe na gaba da zaá gudanar shekara mai zuwa.