1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwar siyasa na ci-gaba a Pakistan

November 11, 2007
https://p.dw.com/p/CABh

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Pakistan ya yiwa wata dokar gyaran fuska don bawa kotunan soji karin ikon yin shari´a ga fararen hula da ake zargi da cin amana kasa ko ingiza mutane su yi bori. Jami´an kasar su ka ba da wannan sanarwa a yau lahadi a daidai lokacin shugabar ´yan adawa Benazir Bhutto ke shirin yin wani maci mai tsawon kilomita 300. Wannan matakin ya zo ne mako guda bayan da shugaba Pervez Musharaf ya kafa dokar ta baci don ba shi ikon yakar sojojin sa kan Islama. To sai dai kawo yanzu dokar ta fi shafar masu sukar lamirinsa musamman lauyoyi da ´yan jarida. A kuma halin da ake ciki Benazir Bhutto ta yi kira ga gamaiyar kasa da kasa da ta kara matsawa shugaba Pervez Musharraf lamba. A wani taro da ta yi da ´yan diplomasiyya na ketare tsohuwar FM ta ce ya zama wajibi Musharraf ya dage dokar ta baci da ya kafa a makon jiya. A wani labarin kuma shugaban Amirka GWB ya yaba da shirye shiryen shugaban Pakistan Pervez Musharraf na dage dokar ta baci cikin wata guda tare da shirya zaben ´yan majalisar dokoki a ranar 15 ga watan fabrairu, wato wata guda bayan yadda aka tsara gudanar da shi da farko.