1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Halitta da Muhalli

Daminar bana ta zo da ambaliya

September 1, 2022

Kama daga Gabas ta Tsakiya da nahiyar Turai zuwa Afirka ta Yamma, ambaliyar ruwa ta haddasa asarar rayuka da dukiyoyi a wannan shekara. A Najeriya, hukumomin kasar sun ce kimanin mutum 500,000 ne lamarin ya tagayyara.

https://p.dw.com/p/4GK7P
Überschwemmung in Nigeria
Hoto: picture alliance/dpa

Jihohi 23 cikin 36 ne dai ambaliyar ta shafa a Najeriyar, inda lamarin ya fi muni a jihohin arewa maso gabashin kasar. Sama da mutum 100 ne dai suka mutu, yayin da wasu 270 suka jikkata, acewar hukumomi. Kawo yanzu mutum 73,000 ne ambaliyar ta raba da gidajensu. Gwamnatin Najeriya ta ce akwai gonaki da ibtala'in na ambaliyar ruwan ya shafa. Galibi dai mutane kan fama da matsalar ta ambaliya a Najeriya a lokutan damina, kama daga watan Mayu zuwa Satumba.