1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damuwa game da halin rashin sanin tabbas a arewacin Mali

Halimatu AbbasJanuary 24, 2013

Ana ci gaba da nuna goyon baya babu kakkautawa ga sojojin Faransa da suka shiga kasar makonni biyu da suka gabata domin yakar 'yan tawaye masu kishin Islama.

https://p.dw.com/p/17Q4F
Hoto: Reuters

To sai dai duk da haka akwai mutane da dama dake tsoron abin da ka iya faruwa ga danginsu dake arewacin kasar ta Mali.

A gaban wani titi dake gaban wani otel mai suna Hotel Lamite wani matashi mai suna Mama Lah da abokansa ke sana'arsu. Su dai wadannan matasa a maimakon jaridu da dai makamantansu da suke tallarsu ga motocin da ke wucewa yanzu sun koma ga sayar da tutocin Faransa.

"Wadannan tutoci inji Mama Lah suna nuni ne ga shigowar sojojin Faransa a kasar. Faransawa sun taimaka mana matuka ainun. Muna sayar da tutocin ne domin nuna gamsuwar mu da haka. Muna matukar farin ciki da cewa yanzu ana yaki da 'yan tawaye."

Akwai 'yan kasar Mali da dama dake nuna farin cikinsu da haka. A kan haka ne ma ba da wata-wata ba suke iya cire CFA 600 kwatankwacin santi 90 na kudin Euro domin sayen 'yar karamar tuta, suke kuma ba da kudin da ya ninka haka domin sayen babbar tuta ta Faransa. Su ma 'yan kasashen waje, walau daga Faransa ko Jamus da Amirka ba a bar su a baya ba wajen jinjina wa Faransa.

Mali Militärintervention
"Kasuwar tutar Faransa ta tashi"-Mamah LahHoto: DW/K. Gänsler

Halin rashin sanin tabbas a arewacin Mali

Ana yin hakan ne kuwa da fatan kawo karshen ta'asar da ke afkuwa a arewacin kasar ta Mali. Oumou Toure mai shekaru 34 da haifuwa tun kusan makonni biyu kenan da ta baro Gao garin haifuwarta ta koma Bamako. Ga dai abin da wannan mata mai 'ya'ya biyu ke cewa game da halin da ake ciki a arewacin kasar.

"Masu kishin Islama ne ke aikata ta'asa saye da shigan burtu. Su ne kuma ke tafiyar da aikin 'yan sanda da kostom da kuma sauran jami'an tsaro.Sune kuma ke tafiyar da aiki a ofishin gwamna. Sun kankane madafun iko. Yanzu in banda su babu kowa a wadannan wurare."

Hada karfi da karfe don yakar 'yan tawaye

To amma yanzu sojojin Mali tare da dakarun Faransa da sojoji 3300 na kasashen ECOWAS sun ja daga domin kau da wannan hali. Kasar Chadi wadda ba mamba ce ta kungiyar ECOWAS ba ita kuma za ta tura sojoji dubu biyu. Akwai kuma kasahen Turai da dama cikinsu har da Jamus da za su ba da taimakon kayan aiki.

Tuni sojojin Faransa suka ba da sanarwar samun nasarar farko . To sai duk da haka ana rashin sanin lokacin da za a dauka ana gwabza wannan yaki . A cewar Alassane Dicko, shugaban kungiyar 'yan kasar ta Mali da aka kora daga matsugunansu ya ce hakan wani abu ne da ka iya janyo rikicin da zai ki ci ya ki cinyewa.

Mali Militärintervention
Oumou Traoré ta zama 'yar gudun hijira a cikin kasarta ta haihuwaHoto: DW/K. Gänsler

"Al'ummar Mali ba ta bukatar yakin da za a dade ana yi. Gaskiya ne cewa yanzu muna yaba wa sojojin Faransa. To amma 'yan kasar Mali na adawa da duk wani aiki da sojojin za su dade suna yi".

Dicko ya kara da cewa daukar matakin soji kadai ba ba zai wadatar ba wajen warware rikicin da ake fama da shi a arewacin Mali.

Ita kuma Oumou Traoré damuwarta ita ce har yanzu akwai wanta da iyalinsa a garin Gao da ba ta san halin da suke ciki ba kasancewar ta shafe kwanaki ba ta samu labarinsu.

Mawallafa: Katrin Gaensler/ Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman

Mun yi muku tanadin sautin wannan rahoto a kasa.