1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan shugabar Laberiya ya sha kaye a zaben kasar

December 23, 2014

Robert Sirleaf da suka fafata da George Weah da yayi fice a fagen kwallon kafa a duniya ya sha kaye a zaben 'yan majalisar dattawan Laberiya.

https://p.dw.com/p/1E9Mx
Ellen Johnson Sirleaf
Hoto: picture alliance / AP Photo

Dan gidan shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta Laberiya Robert Sirleaf ya sha kaye a hannun shahararran tshohon dan wasan kwallon kafar kasar George Weah a zaben majalisar dattawan kasar da ya gudana a karshen makon da ya gabata.

Gidan rediyon Veritas a kasar ta Laberiya ya bada wannan rahoto.

Takarar dai ta George Weah da Robert Sirleaf ta zama takara mafi zafi da ta dauki hankulan al'umma a zaben kasar ta Laberiya wanda aka dage har sau biyu tun daga watan Oktoba saboda fargabar cutar Ebola.

Weah da ya zama dan wasan da yafi kowa bajinta a duniya kamar yadda Hukumar FIFA ta bayyana a shekarar 1995, shi ya kafa jam'iyyar Congress for Democratic Change da ke adawa ya kuma samu kashi 80 cikin dari na kuri'un da aka kada a yankin Montserrado kamar yadda sakamakon zaben na yammacin jiya Litinin ya nunar.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu