1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantaka tsakanin Amirka da Masar

July 11, 2013

Amirka ta ce za ta sake duba irin taimakon soji da take ba wa kasar Masar, mako guda bayan da sojoji suka kifar da zababbiyar gwamnati a kasar.

https://p.dw.com/p/1960n
Hoto: Jacquelyn Martin/AFP/Getty Images

Shugaban kasar Amirka Barack Obama ya bukaci da a sake yin duba ga irin taimakon da Amirka ke ba wa gwamnatin Masar.

Wata sanarwa daga hukumar tsaron Amirka da ke Pentagon, ta bayyana cewa Obama ya ba wa dukkan hukumomin da suke da ruwa da tsaki umurnin su sake duba wannan taimako, sai dai sanarwar ba ta fito fili ta bayyana cewa hakan na da nasaba da juyin mulkin da sojoji suka yi a Masar dinba.

Sanarwar ta zo ne bayan da babban kwamandan sojojin Masar din ya tsallake rijiya da baya, biyo bayan farmakin da wasu 'yan bindiga suka kai wa motarsa a yankin Sinai da ke kan iyakar kasar da yankin Zirin Gaza na Palasdinu.

A hannu guda kuma gwamantin kasar ta Masar na kara daukar matakan murkushe 'yan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da ke zanga-zangar nu na adawa da kifar da gwamnatin tsohon shugaba Mursi, inda ta ba da umurnin kame shugaban kungiyar Mohammed Badie da sauran manyan shugabanninta guda tara bisa zarginsu da laifin tada zaune tsaye.

Tun ranar uku ga wannan wata na Yuli da muke ciki da sojoji suka kifar da gwamnatin Mohammed Morsi, babu wanda ya kara sanya shi a idanunsa. Sai dai kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar ya bayyana cewa, Mursi na nan cikin koshin lafiya a inda ake tsare da shi.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal