1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantaka tsakanin Iran da Amirka

April 12, 2014

Amirka ta bayyana cewa ba za ta baiwa sabon jakadan kasar Iran a Majalisar Dinkin Duniya Hamid Aboutalebi takardar izinin shiga kasar ba wato Visa.

https://p.dw.com/p/1Bgva
Hamid Abutalebi Iran UNO Botschafter
Hoto: Isna

Amirkan dai ta danganta matakin da ta dauka na hana Hamid Aboutalebi izinin shiga kasarta din da muhimmiyar rawar da ta ce ya taka wajen yin garkuwa da Amirkawa a ofishin jakadancin Amirkan a Iran a rikicin shekarun 1979 zuwa 1980 da dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu ta wargaje. Dama dai Shugaba Barack Obama na Amirka na fuskantar gagarumar matsin lamba a kan kada ya bar Aboutalebi ya shiga kasar domin kama aiki a ofishinsa dake birnin New York na Amirkan wanda hakan ke sanya fargabar cewa matakin zai shafi 'yar jaririyar fahimtar junan da aka fara samu tsakanin Iran din daAmirka da ma kasashen yamma a kan shirin makamashin nukiliyar Iran din.

Da yake tabbatar da wannan matsaya da Amirkan ta dauka kakakin fadar gwamnati ta White House Jay Carney ya ce dama saida suka bayyanawa Iran din da kuma Majalisar Dinkin Duniya damuwarsu kan nadin da aka yiwa Hamid Aboutalebi a matsayin sabon jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniyar. Yace a yanzu haka basu da wani zabi da ya wuce na su hana Aboutalebi izinin shiga kasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Mohammed Abubakar