1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel na ziyarar aiki a China

Lateefa Mustapha Ja'afarJune 13, 2016

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci China da ta mayar da hankali wajen mutunta 'yancin dan Adam da kuma tafiyar da al'amura bisa yadda doka ta gindaya.

https://p.dw.com/p/1J5p7
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Firaministan China Li Keqiang
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Firaministan China Li KeqiangHoto: Reuters/W. Zhao

Merkel ta bayyan hakan ne a yayin ziyarar da take yi a kasar China, inda suka tattauna da mahukuntan kasar kan batutuwa da dama ciki kuwa har da sha'anin kasuwanci tsakanin kasashen biyu. Wannan bukata da Merkel ta gabatar ga hukumomin China dai, na zuwa ne dai-dai lokacin da masu rajin kare hakkin dan Adam a kasar ke kokawa kan yadda gwamnatin China ke yin karen tsaye ga hakkin dan Adam din a kasar musamman ma lauyoyi da ke fafutuka wajen ganin an kare hakkin dan Adam.

Angela Merkel da Li Keqiang na China yayin ziyarar da ta kai China
Angela Merkel da Li Keqiang na China yayin ziyarar da ta kai ChinaHoto: picture-alliance/dpa/H. Hwee Young

A bazarar shekarar da ta gabata kadai an kame tare da tsare kimanin mutane 300 da ke wannan fafutuka, batun da ya sanya ake ci gaba da yin Allah wadai da mahukuntan na China yayin da takwarorinta da ke da karfin fada a ji a duniya ke ci gaba da matsa mata lamba wajen ganin ta yi abinda ya kamata kan batun na kare hakkin dan Adam.

Gayyata ga China kan taron kare hakkin dan Adam

A cewar Merkel abu guda da ke da muhimmancin gaske tattaunawar tasu shi ne batun mutunta 'yancin dan Adam. Ta ce zama a tattauna kan wannan batu na da muhimmancin gaske. Ta kara da cewa tana son amfani da wannan damar wajen gayyatar China zuwa Jamus domin halartar taron da za a yi kan kare hakkin dan Adam. Baya ga batun kare hakkin dan Adam, wani abu da shugabar gwamnatin ta Jamus ta tabo shi ne batun bin doka da oda yayin yin dukkan wani al'amari. Merkel ta ce ya na da kyau a ce kamfanonin kasar da ma kuma shirye-shirye da za su yi na hadin gwiwa su kasance an gina su kan yanayin da ya ke kunshe da bin doka da oda.

Da ya ke nasa jawabin yayin wani taro da suka yi tare da bakuwar tasa, Firaministan na China Li Keqiang cewa ya yi Jamus na da muhimmancin gaske ga batu na kasuwanci a China kuma ma yanzu haka Beijing na yin dukannin mai yiwuwa wajen ganin ta kara yaukaka dankon zumunta da ma kasuwanci tsakanin Jamus da takwarorinta na kasashen Turai.

Angela Merkel yayin jawabi ga daliban jami'ar China
Angela Merkel yayin jawabi ga daliban jami'ar ChinaHoto: picture-alliance/AP Images/J. Eisele

Kofofin Jamus a bude suke ga 'yan kasuwa

Li ya kara da cewa Jamus ce ta kan gaba wajen sanya jari a China domin akwai kimanin kamfanonin Jamus guda 10,000 a China. Wannan ya nuna cewar kofofin China a bude suke ga 'yan kasuwa. To sai dai a hannu guda kuma, Firaministan na China ya ce akwai 'yan matsaloli nan da can tsakanin kasarsa da Jamus wanda suka danganci kasuwanci, amma suna bakin kokarinsu wajen ganin lamura sun sauya domin a cewarsa ba sa son ganin an samu wani rikici da ke da nasaba da kasuwanci da kowacce kasa a Turai, ba wai Jamus kadai ba.