1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daraktar tsaron cikin gida a Amirka ta sauka daga muƙaminta

Yusuf BalaOctober 2, 2014

Shugaba Obama na kallon samar da sauyi ga shugabancin sashin kula da tsaron saboda taɓarɓarewar da fannin ke samu.

https://p.dw.com/p/1DOet
Julia Pierson Anhörung zur Sicherheitspanne im Weißen Haus 30.09.2014
Julia Pierson daraktar tsaron cikin gida a Amurka me barin gadoHoto: Reuters/Kevin Lamarque

Daraktar harkokin tsaron Amirka Julia Pierson ta sauka daga muƙaminta ne a jiya Laraba bayan da aka sami gibi a harkokin tsaro da ke da kusanci da shugaba Barrack Obama.

Mis Pierson wacce ke kan wannan muƙami a tsawon watanni 18 ta fuskanci matsin lamba na neman ta sauka daga wannan kujera daga 'yan majalisar dokokin na Amirka tun bayan abun da ya faru ranar 19 ga watan Satumba inda wani da ya taka rawa a yaƙin basasar ƙasar Iraƙi ɗauke da wuka bayan ya shammaci jami'an tsaro da tsallaka katanga ya kutsa kai cikin fadar ta White House kafin wani jami'i da ya tashi daga aiki ya tsaida shi.

Mis Pierson ta faɗawa kwamitin majalisar a ranar Talata cewar ta ɗauki nauyin kuskuren da aka samu wajen harkokin samar da tsaron shugaban ƙasar, saboda haka ne a ranar Larabar ta miƙa takardar sauka daga muƙamin nata bayan wata tattaunawa da sakataren harkokin tsaron cikin gida Jeh Jahnson wanda ya amince da wannan mataki.