1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Darasin Rayuwa: Azumi cikin larura

Abdoulaye Mamane Amadou AH
April 16, 2021

Shirin Darasin Rayuwa na wannan makon ya ji labarin wadanda a shekarun baya ba sa iya kai ga yin azumi daga safe har zuwa yamma, saboda wata larura amma yanzu su na yi.

https://p.dw.com/p/3s6tE
Nigeria Ramadan
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Maikatanga

Al'ummar Musulmi daga ko ina cikin duniya sun wayi gari da watan azumin Ramadan a farkon wannan makon, azumin mai kima da muhimmanci ga al'ummar Musulmin duniya na zuwa jama'a ne da wasu tarin kalubalai, kamar rashin tsaro da rashin kudi uwa-uba da tarin cututtuka ciki har da annobar corona. Wadanda wasu a da ba su yin azumin saboda wata larura amma yanzu su na yi duk da halin da ake ciki.