1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daruruwan mutane a ke sa ran sun halaka cikin teku

Yusuf BalaAugust 28, 2015

An dai kai wasu gawarwaki kimanin 100 zuwa wani asibiti mafi kusa a garin Zuwara a gabar teku a yammacin na Libya.

https://p.dw.com/p/1GNB1
Libyen Flüchtlinge Bergung von Opfern in Zuwara
Gawarwakin wadanda suka rasu bayan jirginsu ya kife a tekuHoto: Reuters/H. Amara

Wasu jiragen ruwa guda biyu makare da fasinjoji sun kife bayan sun baro gabar tekun Libya abin da ya sa rahotanni suka nunar da fargabar cewa daruruwan mutane sun halaka.

An dai kai wasu gawarwaki kimanin 100 zuwa wani asibiti mafi kusa a garin Zuwara a gabar teku a yammacin na Libya, wasu rahotanni kuma suka ce akwai daruruwa da suka bace.

Jami'ai da ke aiki a gabar teku sun bayyana cewa sun sami nasarar ceto wasu mutane 201, sannan akwai wasu da dama da ke makale cikin jirgin da ya nitse. Jirgi na farkon dai na dauke ne da kimanin mutane 50 ya kuma yi kiran neman agaji a jiya Alhamis yayin da daya jirgin kuma ke dauke da fasinjoji 400.

A cewar mazauna garin da aka kai wadannan mutane asibiti mafi yawa bakin haure ne da ke tafiya cikin teku kuma sun fito ne daga kasashen Siriya da Bangaladash da Kudancin Afirka.