1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin kan kisan shugaban kasa

Suleiman Babayo AH
March 21, 2023

A kasar Chadi an yanke hukuncin daurin rai da rai kan mutane fiye da 400 saboda kisan tsohon shugaban kasar Marigayi Idriss Deby Itno a shekara ta 2021.

https://p.dw.com/p/4P28X
Chadi I Marigayi Shugaba Idriss Deby Itno
Marigayi Shugaba Idriss Deby Itno na kasar ChadiHoto: Präsidentschaft von Tschad

A wannan Talata kotu a kasar Chadi ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga 'yan tawaye fiye da 400 da ake zargi da kisan tsohon shugaban kasar Idriss Deby Itno a shekara ta 2021. Mai gabatar da kara na gwamnati ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP haka.

Shi dai mai gabatar da kara Mahamat El-Hadj Abba Nana bai yi karin haske ba kan daurin, amma ya ce akwai wasu mutane 24 da aka sake.

Shi dai Marigayi Idriss Deby Itno shugaban kasar Chadi ya rasa ransa lokacin artabu tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye da suka kunno kai daga kasar Libiya mai makwabtaka. Kuma tun lokacin aka nada dan-marigayin Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin shugaban kasra ta Chadi.