1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Davos: Jan hankali kan ganawar Trump da Kagame

Ramatu Garba Baba
January 26, 2018

Shugaban Amirka Donald Trump a wannan Juma'a ya gana da takwaransa na kasar Ruwanda Paul Kagame a karon farko bayan kalaman wulakancin da ake zarginsa da furtawa kan kasashen yankin Afrika da Haiti da El Salvador.

https://p.dw.com/p/2rZtW
Weltwirtschaftsforum 2018 in Davos | Dinner CEO's & Donald Trump, Präsident USA
Hoto: Reuters/C. Barria

Shugabanin biyu sun gana ne a gefen taron tattalin arziki na duniya da ke gudana a birnin Davos, bayan ganawar dai babu wanda ya ce uffan kan kalamai marasa dadi da ake zargin Trump da furtawa akan kasashen yankin Afrika, amman kowannen su ya yaba da ganawar da suka ce na da mahinmanci ga ci gabansu.

A can baya an zargi shugaban na Amirka da bayyana wasu kasashe da suka kunshi Afrika da El Salvador da Haiti a matsayin wulakantattu, inda ya ce bai ma ga dalilin da ya sanya kasarsa ke karbar mutanen da suka fito daga wadannan kasashen ba, duk da cewa daga baya ya musanta cewa ya ambaci wadannan kasashe da wannan sunan.

A yayin jawabinsa na wannan Juma'ar a gaban taron na Davos ma, wasu sun yi wa Trump ihu bayan da ya soki wasu kafafofin yada labarai da ya zarga da iya yada labaran karya. Ana sa ran shugabanin kasashen Afrika za su yi nazari kan kalaman na Trump a babban taron AU da za a soma a wannan Lahadi a kasar Ethiopia: