1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dawowar zaman lafiya a Jihohin Borno da Yobe

Usman ShehuJanuary 16, 2013

Rahotanni su ka ce, zirga-zirgar jama'a ta fara dawowar kamar da, a jihohin Borno da Yobe, waɗanda suka daɗe suna fama da tashin hankali

https://p.dw.com/p/17LGI
Titel: DW_Nigeria_Integration-online2 Schlagworte: Maiduguri, Zentralmoschee Fotograf: Katrin Gänsler Aufnahmedatum: 20. Februar 2008 Aufnahmeort: Maiduguri, Nigeria Bildbeschreibung: Im Zentrum von Maiduguri wird die neue Zentralmoschee gebaut
Hoto: Katrin Gänsler

A iya cewa dai jihohin Borno da Yobe sune ke kan gaba a Najeriya da suka fi fama da tashe-tashen hankulan da ake dangantawa da ƙungiyar nan mai gwagwarmaya da makamai don kafa shari'ar musulunci da aka fi sani da Boko Haram, inda harkoki suka tsaya cik, mutane kuma suka kaurace wa garuruwan.

To amma yanzu haka abin ya canza, don kuwa al'ummar jihohin musamman manyan garuruwan Maiduguri da Damaturu da Potiskum sun shida min cewa hada-hadar kasuwancin da harkokin yau da kullum sun fara komawa kamar yadda suke a baya. Malam Muhammad wani mazaunin garin Potiskum ne a jihar Yobe, ya shaida min halin da ake ciki a garin a halin yanzu a wata tattaunawa da muka yi da shi ta wayar tarho.

Kashim Shettima, Gouverneur von Borno State, Nigeria Usman Shehu, 15.06.2011, Maiduguri / Nigeria
Kashim Shettima, gwamnan jihar Borno.Hoto: DW

Ya ce "godiya ga Allah, zaman lafiya ya fara komowa kamar yadda yake a baya, mutane suna kasuwancin su ba tare da tsangwama ba, kasuwanni da makarantu sun koma ayyukan su, yanzu haka da nake magana da kai ina ganin manyan motoci cike da mutane suna shigowar da mutane da suka bar gidajensu don yin gudun hijira. Sama da sati uku zuwa wata daya kenan, ban ji wani tashin hankali ba"

Haka al'amarin yake a garin Maiduguri dake zama babbar tunga ko hedkwatar kungiyar gwagwarmayar, inda nan ma ake ganin al'ummomin da a baya suka tsere daga garuruwan suna komawa gidajen su, duk da cewa dai suna dar-dar da fargabar cewa watakila anan gaba lamarin ka iya sake rincabewa. Malam Isma'il Abubakar wani ne da na gamu da shi wanda ya zo Gombe daga Maiduguri ya shaida min cewa yanzu kam tubarkalla, al'amura sun fara dai dai tuwa a garin da abaya ake masa kirari da gidan zaman lafiya.

some childrens ranging from five years to eight hawking goods from car to another in one of the filling stations in Maiduguri city, sept 29th, 2005. I ibrahim sani from Africa/Nahost, Haussa Dept, hereby authorize Dw- Radio to use the above mentioned pictures in their Bild Datum bank.
Wasu yara ke talla a birnin MaiduguriHoto: DW

Na ziyarci tashoshin mota dake sufurin mutane zuwa garuwan Maiduguri da Damaturu da Potiskum, na kuma shaida mutane na cika motocin zuwa garuruwan, ko dai don kasuwanci ko ziyarar ‘yan uwa da abokan arziki ko kuma komawa gidajen su. Wannan yanayi ya farantawa al'ummar yankin Arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda Alhaji Ibrahim Isa wani mazaunin Gombe ya shaida min.

Oliver Doeme Dashe, Bischof von Maiduguri / Nigeria Usman Shehu, 15.06.2011, Maiduguri / Nigeria
Oliver Doeme Dashe, Bishop mai kula da yankin MaiduguriHoto: DW

Yayinda jami'an tsaro ke danganta samar da zaman lafiyar da matakan ba sani ba sabo da suka dauka wanda acewar su ya kai ga cin karfin mayakan kungiyar gwagwarmayar, su kuma al'umma na ganin Allah ne ya karbi addu'o'in su ba wai kokarin jami'an tsaron ba. Kokarin da na yi don jin ta bakin gwamnatocin jihohin kan matakan da za su dauka na dorewar zaman lafiya yaci tura, don kuwa wayoyin jami'an da na buga wasu sun shiga ba'a dauka ba, wasu kuma suna rufe.

Mawallafi: Al-Amin Sulaiman Muhammed

Edita: Usman Shehu Usman