Dawowar zaman lafiya a Mubi
A 2014, 'yan Boko Haram sun mamaye Mubi a Arewa maso gabashin Najeriya na tsawon makonni. Sai dai duk da korar 'yan ta'adda da aka yi- har yanzu ana fama da shakku. Abin da Kiristoci da Musulmi ke son canzawa tare.
Damuwa kan makomar siyasa
Garin Mubi na jihar Adamawa ta Najeriya na tsakiyar yakin neman zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 16 ga Fabirairu. Sai dai 'yan siyasa ba sa magana game da abu guda, wato yadda mazauna garin ke tunawa da mamayar da 'yan Boko Haram suka yi masu a shekarar 2014.
Bincike ba ya tasiri sosai
A cikin watannin Oktoba da Nuwamba na 2014, mayakan kungiyar sun yi makonni a cikin garin Mubi. A cikin watan Nuwamba 2017 da Mayu 2018, sun kai munanan hare-hare a masallatai biyu da kuma kan wata kasuwa inda gwamman mutane suka mutu. Wannan ya faru duk da yawan 'yan sanda da sojoji a kewayen birnin.
Agaji a lokacin da ake bukata
Lokacin da Boko Haram ta karbe iko da Mubi, Fatima Sharfadeen, mai shekaru 16 na cikin makaranta. "Na dauki 'yan uwana kuma na sa su a cikin motar makaranta," in ji ta. Daga bisani sai ta tsere tare da iyayenta zuwa kasar Kamaru. Ba za ta taba manta da irin tsoron da ta ji a wannan lokaci ba.
Rusa bankuna da rikicin ya yi sanadi
An tunatar da dalibai game da ayyukan ta'addanci da aka fuskanta a duk fadin garin Mubi. Mayakan Boko Haram sun lalata wasu bankuna wadanda ba a sake gina su ba har i zuwa yanzu.
Hare-hare a kan majami'u 337
An yi ta boyewa a ginshikan majami'u. An kiyasta cewa a arewacin jihar Adamawa an kai hare-haren a kan wuraren ibada 337. Ya zuwa yanzu, yawancin Kiristocin da suka kaurace wa matsugunansu sun fi nuna damuwa. Ba a san wanda ya hada kai da Boko Haram ba, a cewar su.
Nasarar kawar da shakku
Tsamin dangantaka tsakanin Kirista da Musulmi zai iya kawo tabarbarewar zamantakewa a cikin birnin na Mubi. Don kawar da shakku bayan kwato Mubi ne Yusuf Yaro, shugaban majalisar Musulmi a Mubi ta Kudu (hagu), da kuma limamin Katolika, Alexander Miskita William suka hada hannu. Imam ya shafe shekaru yana ziyartar majami'ar St. Andrew.
Dagewa don daidaita al'amura
Wadannan matakai ne masu muhimmanci, in ji Fasto Daniel Doyi na Cocin E.Y.N. (majami'ar Brethren) da Shugaban cibiyar tabbatar da zaman lafiya tsakin Kirista da Musulmi. "Kiristoci da Musulmi masu matsakaicin ra'ayi suna sake karfafa huldarsu a hankali," in ji shi, amma ya ce, "Mubi bai daidaita yadda ya ke a da ba"
Ya kamata gwamnati ta goyi bayan tattaunawa
Sake gina majami'u, kamar na E.Y.N a barikin 'yan sanda zai taimaka wajen cimma manufa. Sai dai Fasto na ganin laifin gwamnatin. "Har zuwa yanzu, kungiyoyi masu zaman kansu ne kawai suka damu da tattaunawa tsakanin mabiya addinai daban-daban," in ji Doyi.
NIREC na samar da sulhu
Muhammad Abbas, wanda ya ke aiki a karamar hukumar Mubi ta Arewa, bai yarda da wannan zargi ba. Ya nuna cewar majalisar sansanta rigingimun addini (NIREC) na aikinta. "Tana wa'azi kan zaman lafiya, mutane kuma sun san da hakan."
"Boko Haram ta yi wa addini lahani"
A cewar Fasto John Musa, shugaban kungiyar Kiristan Najeriya (CAN) reshen Mubi ta Kudu, samun ilimin addini na da muhimmanci. "Islama addini na zaman lafiya kamar yadda Kiristanci yake. Kungiyar Boko Haram dai ta zalunci addini ne kawai.
Kiristoci na ziyartar Musulmi
Wannan zurfin tunani ya sa Kiristoci da Musulmi farfado da dangantakar da ke tsakaninsu. "Misali mafi kyau shi ne Kiristoci su dawo cikin masu tafiyar da majalisar Musulmi," in ji Imam Yaro, wanda ya shirya abubuwan da dama da Fasto Musa.
Ilimin zaman lafiya ga manyan gobe
Ga yara da matasa: Ya kamata su girma tare ba tare da wani bambanci ba. Wannan ne ya sa aka samar da kungiyar zaman lafiya a makarantar Fatima Sharfadeen tare da Noah Amos Drambi mai shekaru 16 da haihuwa da kuma Jibrilla Garba. Mataimakin Shugaban Camp, tana tattaunawa a kan wani sabon mataki da ke tabbatar da muhimmancin zaman lafiya a rayuwa.