1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Diendere ne shugaban mulkin soji a Burkina

Mouhamadou Awal BalarabeSeptember 17, 2015

Sanarwar sojojin da suka yi juyin mulki ta nunar da cewar Janar Gilbert Diendere na hannun daman Compaore ne ya zama shugaban mulkin soji a Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/1GY0N
Burkina Faso Ouagadougou Präsidentenpalast
Hoto: picture-alliance/dpa/L. Koula

Sojojin da suka yi juyin mulki a Burkina Faso sun nada Janar Gilbert Diendere a matsayin wanda zai jagorancin gwamnatin mulkin sojin wannan kasa ta yammacin Afirka. Cikin wata sanarwa da suka karanta a talabijin din kasar sun bayar da umurnin rufe iyakokin Burkina Faso na kasa da kuma sama, tare da kafa dokar hana fitar dare.

Da ma dai dogaran fadar shugaban kasa da suka yi juyin mulkin sun riga sun bayyana cewar sun rusa gwamnati da kuma majalisar rikon kwarya da aka kafa a watanni baya. Sannan kuma suna ci gaba da garkuwa da shugaban rikon kwarya Michel kafando da kuma firaministan na Burkina Faso Isaac Zida.

Janar Diendere dai aboki ne ga shugaba Blaise Compaore wanda guguwar neman sauyi ta yi awon gaba da mulkinsa. Ya na daga cikin wadanda suka mara wa Compaore baya wajen hambarar da gwamnatin Thomas Sankara a 1987. Shi din ne kuma ya shugabanci rudunar dogoran da ke tsaron shugaban kasa har lokacin da aka tsigeshi daga wannan mukami makonni kalilan bayan da Compaore ya sauki daga mulki.