1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Djibouti ta kaddamar da babbar tashar kasuwanci

Ramatu Garba Baba
July 5, 2018

A wannan Alhamis aka kaddamar da wata katafariyar tashar kasuwanci a kasar Djibouti, tashar ta na da fadin hecta 240 wanda bayan kammala ta, za ta kasance mafi girma a nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/30tfI
Dschibuti
Hoto: AP

A jawabinsa yayin kaddamar da tashar, shugaban kasar Ismael Omar Guelleh ya yaba da shirin da kasar ta jagoranci samarwa tare da wasu kamfanonin China uku, shugaban ya ce tashar za ta yi tasiri wajen habbaka harkokin kasuwanci, kasancewarta babbar cibiya ta kasuwanci da ke hada kasashen yankin kahon Afirka.

 Ana fatan ganin, wannan zai iya janyo kamfanoni dama masu son zuba jari daga kasashen yamma. Shugabanin kasashen Somaliya da Habasha da na Ruwanda da Sudan da suka hallarci bikin, sun ce nasara ce babba ga gwamnatoci dama al'ummar yankin baki daya.