1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Djotodia ya yi murabus a kokarin warware rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

January 10, 2014

Taron shugabannin Kungiyar Kasashen Tsakiyar Afirka ya ayyana murabus na shugaban wucin gadin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a kokarin lalubo mafita ga rikicin kasar.

https://p.dw.com/p/1AouY
Zentralafrikanische Republik Michel Djotodia
Hoto: Getty Images/Afp/Eric Feferberg

Bayan tsawon kwanaki biyu suna tattaunawa a birnin Ndjamena na kasar Chadi, shugabannin kasashen yankin tsakiyar Afirka sun gayyato masu ruwa da tsaki wajen tafiyar da harkokin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wadanda suka hada da 'yan majalisar dokokin kasar, da shugabannin addini da na kabilu domin yin wata ganawar sirri a tsakanin su.

Jim kadan bayan ganawar ce kuma, sakatare janar na kungiyar kasashen yankin, Ahmat Allami ya sanar da murabus na shugaban wucin gadin kasar Michel Djotodia, tare da mika ragamar jagorancin Jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya zuwa ga hannun shugaban majalisar, kafin zaban sabon shugaban wucin gadi cikin wa'adin makonni biyu.

Zentralafrikanische Republik Michel Djotodia Verhandlungen Ndjamena Tschad
Taron kasashen yankin tsakiyar AfirkaHoto: Brahim Adji/AFP/Getty Images

A tsokacin da yayi dangane da wannan ci-gaban, shugaban Chadi, Idriss Deby Itno, wanda har wayau ke zama shugaban kungiyar, ya bayyana kudirin shugabannin yankin na tallafa wa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin warware rikicin kasar, wanda ya janyo mutuwar mutane da dama, tare da tilastawa wasu dubbannin kuma tserewa daga matsugunansu.

Mawallafi : Abdourazak Garba Baba Ani
Edita : Saleh Umar Saleh