1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Halitta da Muhalli

Dokar yaki da gurbata muhalli a Afirka ta Kudu

Gazali Abdou Tasawa
May 27, 2019

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sanya hannu kan wata sabuwar dokar yaki da gurbata muhalli a kasar wacce ta tanadi dora haraji kan masu fitar da gurbatacciyar iskar gaz

https://p.dw.com/p/3JCSL
Südafrika Präsident Cyril Ramaphosa
Hoto: AFP/M. Spatari

Dokar wacce za ta soma aiki daga ranar daya ga watan Yuni mai zuwa ta tanadi dora haraji na Euro bakwai da santi 40 a kan kowane ton daya na gurbatacciyar iskar da injina ke fitarwa. 

Gwamnatin Afirka ta Kudun ta ce ta dauki wannan mataki ne domin rage fitar da gurbatacciyar iskar wacce ke yin illa ga rayuwar dan Adam da ma muhalli baki daya. Afirka ta kudu dai na a matsayin ta farko wajen gurbata muhalli a Afirka kana ta 14 a duniya baki daya.

Tuni dai Kungiyoyin da ke fafutikar kare muhalli na duniya irin su WWF da Greenpeace suka jinjina wa Shugaba Ramaphosa kan wannan mataki da ya dauka, ko da shi ke cewa daga nata bangare kungiyar Greenpeace na ganin harajin da aka dora ya yi kadan wajen tsoratar da manyan kamfanonin da ke yada gurbatacciyar iskar a kasar.