1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na neman zama tsumman zani

October 22, 2018

Kura da lafa a jihar Kadunan Najeriya, bayan dokar hana zirga-zirga na tsawon sa'o'i 24 da gwamnatin jahar ta sanya da nufin dakile karuwar tashe-tashen hankula da suka janyo asarar rayuka da kone-konen dukiyoyi.

https://p.dw.com/p/36wkP
Nigeria Protest gegen Benzinpreise
Hoto: dapd

Gwamnatin jihar ta Kaduna dai ta dauki matakin sanya dokar ne domin tabbatar biyo bayan barkewar wani tashin hankalin a garin Kujama, inda wasu masu tayar da zaune tsaye suka fara farwa al'umma da sare-sare. Dama dai wasu yankuna a cikin Kadunan na fama da matsalar tabarbarewa tsaro, wanda akan haka ne gwamnatin ta baza jami'an tsaronta a koina.  Tuni rudunar 'yan sanda ta baza jam'an tsaro dan tabbatar da bin doka da oda. Da yake karin haske kan matakin na gwamnati, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kadunan CP Ahmed Abdulraman ya ce daukar wannan doka ya zamo wajibi bisa la'akari da ganin yadda wasu miyagun mutane suka fara cin zarafi da daukar doka a hannnusu, kuma lallai lokaci ya yi da kowa da kowa zai tashi tsaye domin ganin an dauki matakan shawo kan matsalar tashe-tashen hankulan. Rahotannni sun nunar da cewa kama sarkin Kabilar Adara na zaman guda daga cikin dalilan da suka sanya matasan gudanar da wata zanga- zanga da ta juye zuwa tarzoma.

Babu shakka dai wannan doka ta samu tasiri sosai, domin kuwa dukkanin jami'an tsaro wadanda suka hada da sojoji da 'yan sanda da kungoyin tsaro na fararen hula duk sun hada kai acewar kwanmishina 'yan sandan, wanda ya ce ba za su taba amincewa da rashin tsaro a cikin wannan kasar ba, saboda haka lallai akwai bukatar tabbatar da bin doka da Oda a wannan lokaci domin kaucewa duk wata barazanar tabarbarewar tsaro a cikin jihar. Wannan rikicin dai ya samo asali ne sakamakon rashin jituwa tsakanin matasan kabilar Adara da Hausawa a kasuwar magani, ya kuma janyo asarar rayukan mutane 55 da dimbin dukiyoyi.