1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Afirka na fuskantar karancin ruwan sha mai tsafta

Abdourahamane Hassane
March 19, 2019

Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai kamar mutane biliyan biyu da 'yan ka, a duniya wadanda ba sa samun ruwa mai tsabta na sha.

https://p.dw.com/p/3FIzQ
Trinkwassser an Schule in Burundi
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Schulze

Rahoton wanda hukumar illmi da raya al'adu ta MDD, UNESCO ta bayyana, a jajibirin ranar da MDD ta ware ta ruwa a duniya a ranar 21 ga watan Maris, ta ce mafi yawan wadanda lamarin ya shafa na zaune ne a kasashen Afirka. Yayin da wasu mutanen miliyan 57  a nahiyar Turai da Amirka ta arewa ba su da hanyoyin samar da ruwan shan mai tsabFa a gidajensu.