1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya na kunshe da makafi dubu 36 a shekara ta 2015

Gazali Abdou Tasawa
August 3, 2017

Sakamakon wani rahoton bincike da aka wallafa a wannan Alhamis ya nunar da cewa mutane miliyan 36 na fama da larurar makanta a duniya a shekara ta 2015.

https://p.dw.com/p/2hbvC
USA Stevie Wonder und Tomeeka Robyn Bracy
Hoto: picture alliance/newscom/J. Ruymen

Sakamakon wani rahoton bincike da aka wallafa a wannan Alhamis ya nunar da cewa mutane miliyan 36 na fama da larurar makanta a duniya a shekara ta 2015. Sai dai rahoton wanda jaridar da ke wallafa labaran da suka jibanci kiwon lafiyar dan Adam ta The Lancet Global Health ta wallafa ya ce adadin makafin zai nunka zuwa gida uku nan zuwa shekara ta 2050. 

Kazalika rahoto ya ce mutane miliyan 217 suka fuskanci matsakaiciyar matsalar gani a shekarar ta 2015, matsalar da ita ma za ta nunka gida uku wato zuwa mutun miliyan 588 a shekara ta 2050. Bugu da kari rahoton ya bayyana cewa mutane sama da miliyan dubu ne suka yi fama da kankanan matsalolin gani da ke da nasaba da karuwar shekaru a shekarar ta 2015. 

Matsalar ta fi kamari a cewar rahoton a kasashe masu tasowa na nahiyar Afirka da Asiya, kana ta fi shafar mata fiye da maza inda kashi 56 daga cikin dari na makafin duniya ya kasance matan. Sai dai masu binciken sun bayyana cewa matsalar na iya ja da baya idan kasashe sun dage wajen saka wadatattun kudade a fannin kula da lafiyar al'umma.