1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

DW na kara samun tagomashi a duniya

Abdullahi Tanko Bala
June 5, 2018

Shugaban Deutsche Welle Peter Limbourg ya jinjinawa bunkasar tashar wajen kai wa ga mutane fiye da miliyan 150 a duniya ta radiyo da talabijin da Intanit da kuma hanyoyin sada zumunta na zamani a cikin harsuna 30.

https://p.dw.com/p/2yzV7
Mitarbeiterversammlung 2013 in Berlin Peter Limbourg
Hoto: DW

Tashar ta fara yada shirye shiryenta ga kasashen duniya a shekarar 1953 da gagarumin kalubale inda ta fara da yada shiri ta gajeren zango da harshen Jamusanci kawai amma a yanzu ta bunkasa da fannonin sadarwa da dama cikin harsuna 30 yayin da kuma shirye shiryen ke isa ga mutane fiye da miliyan 150 a fadin duniya a kowane mako ta radiyo da talabijin da kuma kafar Internet da hanyoyin sada zumunta na zamani.

Shugaban Tashar ta DW Peter Limbourg yace bama kawai tashar tana bada sahihan labarai masu inganci bane kadai ta kuma dage wajen yaki da labaran karya da ke neman zama ruwan dare a wannan zamani. 

"Yace tashar Deutsche Welle tana isa ga mutane masu dumbin yawa a fadin duniya fiye da yadda ake tsammani, ta kuma sami martaba da daukaka a cikin gida a nan Jamus wanda ya kasance abin farin ciki da alfahari. Muna fatan cigaba akan haka tare da shawo kan farfaganda da fallasa labaran karya. Burin mu shine baiyana tsantsan gaskiyar lamura a Jamus da nahiyar Turai baki daya.