1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ebola da gasar Africa Cup sun dauki hankalin Jamusawa

Mohammad Nasiru AwalNovember 14, 2014

A wannan makon jaridun na Jamus sun mayar da hankali a kan cutar Ebola da kace nace da ta janyo ga gasar cin kofin kwallon kafar kasashen nahiyar Afirka a farkon shekarar badi.

https://p.dw.com/p/1Dmtf
Hoto: picture-alliance/dpa/N. Bothma

A labarin da ta buga jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi kasancewa gasar cin kofin kwallon kafa ta Africa Cup na zaman muhimmiyar kafar samun kudi ga Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta nahiyar Afirka CAF, za a gudanar da gasar duk da annobar cutar Ebola. Wata sanarwa da Hukumar ta CAF ta bayar a wannan Jumma'a ta ce kasar Equitorial Guinea za ta dauki nauyin shirya wasan na shekara mai zuwa, bayan da kasar Marokko, wadda ya kamata ta dauki nauyin wasannin ta ce a kai kasuwa saboda fargabar cewa ana iya shigo mata da kwayoyin cutar Ebola cikin kasar. Jaridar ta ce dalilan da Marokko ta bayar ba su da karfi sosai, amma ko da mutum daya ne aka kwantar asibitin kasar saboda harbuwa da kwayar cutar, to zai yi wa Marokko mummnar illa. Domin kasar ta dogara ga masu yawon bude ido daga ketare, wadanda kuwa ba za su je kasar ba matukar an sanya ta a jerin kasashen da aka samu Ebola a cikin su.

Hannun agogo ya koma baya ga magance Ebola

Murna ta koma ciki inji jaridar Die Tageszeitung tana mai mayar da hankali ga sabbin mace-macen da aka samu a kasar Mali dangane da Ebola.

Dousseyni Daou Hospital in Kayes Mali Ebola Kind
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Baba Ahmed

Ta ce an ga alamun shawo kan cutar a kasar da ke yankin Sahel, amma mutuwar wani limami ta shammaci hukumomin birnin Bamako. Hakika a baya masana na duniya da ma na kasar sun kyautata fatan cewa Mali ba za ta fuskanci matsalar Ebola ba, saboda kwararan matakan da ta dauka biyo bayan mutuwar wata yarinya sanadin cutar Ebola bayan ta shiga Mali daga Guinea. To amma tun makonni biyu da suka wuce an rika samun 'yan kasar musamman wadanda ke komawa Mali daga Guinea, da suka harbu da kwayoyin cutar. Wannan lamari ya sake sanya fargaba a fadin kasar baki daya.

Karuwar hare-hare kan makarantu a Najeriya

Nigeria Anschlag Bombe Explosion Selbstmordanschlag
Hoto: picture alliance/AP Photo

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine ta yi tsokaci ne a kan tashe-tashen hankulan da suka ki ci suka ki cinyewa a arewacin Najeriya.

Ta ce har yanzu 'yan bindiga a Najeriya na ci gaba da cin karensu babu babbaka, inda a wannan karon 'yan makaranta da dama suka rasu a wani harin kunar bakin wake da aka kai kan wani dakin taron na wata makarantar sakandare da ke garin Potiskum. Hakan dai ya zo ne yayin da makonni bayan nan gwamnatin Najeriya ta yi ta nanata nasarar da aka samu a tattaunawar tsagaita wuta da kungiyar Boko Haram, batun da kungiyar ba ta tabbatar ba. Kuma tun sannan hare-haren da 'yan ta'adda ke kaiwa sun karu. Shugaba Goodluck Jonathan wanda a ranar Talata a hukumance ya kaddamar da kamfen sake tsayawa takarar neman kujerar shugabancin kasar a zaben shekarar 2015, ya mika jajensa ga wadanda lamarin ya shafa kuma ya yi alkawarin zakulo masu hannu a wannan ta'asa. To sai dai ba wanda ya yarda da irin wadannan alkawura kasancewa a baya ma an yi amma ba a gani a kasa ba.