1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ebola-mutuwa ta biyu a kasar Mali

November 12, 2014

Mahukuntan kasar Mali sun tabbatar da mutuwar wata jami'ar jinya da ta kamu da Ebola bayan ta kula da wani mai dauke da cutar da ya fito daga kasar Gini a wani asibiti dake Bamako .

https://p.dw.com/p/1DldL
Hoto: picture-alliance/AA/Mohammed Elshamy

Wannan dai shine ya kawo adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar ta Ebola a kasar Mali zuwa mutane biyu, bayan da wata yarinya mai kimanin shekaru biyu da kakarta ta dauko ta ita ma da ga Gini ta ce ga garinku nan sakamakon cutar ta Ebola. Sai dai rahotanni sun nunar da cewa mutuwar jami'ar jinyar ba ta da nasaba da mutuwar yarinyar 'yar shekaru biyu, wadda ta mutu a kasar cikin watan Oktoban da ya gabata.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu