1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ebola ta fara lafawa a kasar Laberiya

October 29, 2014

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ana samun lafawar cutar Ebola

https://p.dw.com/p/1De92
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Baba Ahmed

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa an fara samun lafawar sabbin kamuwa da cutar Ebola a kasra Laberiya da ke zama wadda cutar tafi ta'adi.Mataimakin shugaban hukumar Bruce Aylward ya ce an tabbatar da samun raguwa na mutanen da cutar take kamawa a Laberiya.

Amma ya nemi taka tsantsan da kara jan damara wajen kawar da cutar. Hukumar Lafiyar ta duniya ta ce cutar ta Ebola ta kama fiye da mutane 10,000 yayin da ta hallaka kusan 5,000 galibi a kasashen Gini, da Laberiya da kuma Saliyo.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe