1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ebola tana yaduwa a Najeriya

August 14, 2014

Mutane 11 aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a Tarayyar Najeriya

https://p.dw.com/p/1Cukq
Hoto: Reuters

Najeriya ta tabbatar da cewa mutane 11 a cikin kasar suna dauke da kwayar cutar Ebola, ciki har da likitan da ya duba dan kasar Liberiya wanda ya shiga da cutar cikin kasar.

Ministan lafiya na Najeriya Onyebuchi Chukwu ya shaida wa taron manema labarai a birnin Abuja cewa, akwai mutane kusan 170 da ake kula da su na yiwuwar ko suna dauke da cutar saboda yadda suka yi ma'amala da wadanda aka tabbatar sun harbu da cutar ta Ebola.

Tuni kamfanin Aliko Dangote wanda shi ne mutumin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, ya bayar da gudunmawar dala milyan 150 domin dakile cutar da Ebola, wadda take yaduwa sannu a hankali a cikin kasar ta Najeriya. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce wannan karo aka samu yaduwar cutar mafi muni a yankin na yammacin Afirka, inda ta hallaka fiye da mutane dubu a kasashen Saliyo, da Gini, da Liberiya da kuma Najeriya inda mutane uku suka hallaka.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal