1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Guinea-Bissau ya yi kamari

Salissou Boukari LMJ
November 8, 2019

An kammala zaman taron kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO, wanda ya tattauna batun rikicin siyasa a kasar Guinea-Bissau a Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/3Sidf
José Mário Vaz
Shugaban kasar Guinea-Bissau José Mário VazHoto: DW/B. Darame

Rikicin dai ya samo asali ne tun bayan da shugaban kasar ta Guinea-Bissau da wa'adin mulkinsa ya kawo karshe, ya sa kafa ya shure yarjejeniyar da aka cimma, inda ya ce ya kori firaministan da majalisar dokokin kasar da ma kungiyar ECOWAS suka amince da shi tare da nada wani firaministan na daban. Sai dai kuma kungiyar ta ECOWAS ta ce ko kadan hakan ba zata sabu ba yayin da 'yan kwanaki ne suka rage a kai ga zaben shugaban kasa a kasar ta Guinea-Bissau.

Kokarin samo mafita a rikicin Guinea-Bissau

Da yake jawabi yayin bude taron gaggawa da ECOWAS din ta kira, shugaban Jamhuriyar Nijar wanda kuma shi ne shugaban kungiyar, Issoufou Mahamadou ya yabawa takwarorinsa shugabannin kasashe da suka halarci wannan zama domin shawo kan rikicin kasar ta Guinea-Bissau, inda ya ce a shekara ta 1999 an saka batun kare afkuwar rikici da samar da zaman lafiya mai dorewa a cikin kasashe, sannan kuma aka kara da batun da ya shafi dimukuradiyya da gudanar da kyakkyawan mulki a ranar 21 ga watan Disamba na 2001 dan ganin kasashe mambobin kungiyar ta ECOWAS sun kasance masu bada misali na gari wajen harkokin mulki kuma wannan yanayi na kasar Guinea-Bissau ya saba wa tsarin kungiyar.

Guinea-Bissau Delegation ECOWAS
Tawagar ECOWAS a Guinea-Bissau domin shawo kan rikicin kasarHoto: DW/B. Darame

A wurin wannan taro dai an samu halartar shugabannin kasashen Côte d'Ivoire da Sénégal, da Ghana da Laberiya da Saliyo da Togo da Benin da kuma Nijar mai masaukin baki. Sannan akwai mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo.

Bukatar dakatar da rikici a Guinea-Bissau

A jawabinsa, shugaban hukumar kungiyar ta ECOWAS Jean-Claude Kassi Brou ya yi waiwaye ne adon tafiya wajen tunatar da mahalarta taron matakan da kungiyar ta dauka a babban zaman taronta karo na 55 da ya gudana a watan Yuli a birnin Abuja na Tarayya Najeriya na  bai wa kasar ta Guinea-Bissau talafin kudi har dalar Amirka miliyan daya da rabi domin shirya zaben. A karshen wannan zaman taro, shugabannin kasashe da na gwamnatoci na ECOWAS sun yi Allah wadai da matakin da shugaban Guinea-Bissau José Mário Vaz ya dauka na bijirewa tsarin da aka yi na sulhu, tare da yin kira ga jami'an tsaron kasar da su tsaya a matsayinsu, kana ta bukaci firaministan da shugaba Vals ya nada da ya yi murabus ko kuma ya fuskanci hukunci na takunkumi. Shugabannin kasashen Cote d'Ivoire da Gambiya da Najeriya da kuma shugaban Nijar wanda shi ne shugaban kungiyar ta ECOWAS, za su mika sakamakon wannan taro ga shugaban kasar ta Guinea-Bissau José Mario Vaz.